Rasuwar Tauraruwa Wasila ta kawo jimami da muhawara kan rayuwar aurenta da Jarumi Ciroma

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Masu hikima kan ce, “Allah Ya raba mu da ranar yabo.” Ba wai yabo ba ne ake gudu, illa dai saboda galibi ranar da mutum ya fi samun yabo ita ce ranar da ya riga ya bar duniya ko kuma ya bar wajen da maganar tasa ta taso. A lokacin da mutum yake raye, mutane kan yi saurin ganin kuskurensa, su yi masa hukunci, su zarge shi, ko ma su ɗora masa laifukan da ba a tabbatar da su ba. Amma da zarar mutuwa ta auku, zuciyoyi kan fara narkewa, harsuna su fara sassautawa, mutane kuma su fara tuna alheran da suka manta da su tun yana raye.

Wataƙila wannan ne sirrin da ya sa ake cewa, mutuwa ita ce wa’azi mafi girma, domin tana rushe katangar fushi, tana karya girman kai, tana kuma tilasta wa mutane sake kallon abubuwan da suka faru da idon adalci maimakon na son rai. Sau da yawa, kalmomin da mutum ya kasa sa mutane su fahimta yana raye, su ne suke samun masauki a zukata bayan ya tafi.

Hakan ne ya sake bayyana a cikin lamarin Marigayiya Wasila Isma’il, fitacciyar jarumar Kannywood da ta rasu a ranar 24 ga Mayu, 2026, tana da shekaru 46 bayan fama da rashin lafiya. 

Rasuwarta ba kawai ta jefa masoya da abokan sana’arta cikin jimami ba, ta kuma sake buɗe wani tsohon babi na rayuwarta, wanda mutane da dama suke ganin bai taɓa rufewa gabaɗaya ba. 

Kafin a san ta da cece-kucen da suka biyo bayan rabuwar aurenta, Wasila Isma’il ta kasance ɗaya daga cikin taurarin da suka haska sararin Kannywood a farkon shekarun bunƙasar masana’antar.

Ta fara fitowa a fim a shekarar 1998 cikin ‘Jinin Masoya’, amma a shekarar 1999 ne ta sauya alƙiblar rayuwarta bayan fitowarta a fim ɗin ‘Wasila’, wanda aka shirya tare da shahararren jarumi Ali Nuhu. Abin sha’awa, fim ɗin ma tun farko an sanya masa suna Jamila, amma ita kanta Wasila ta nemi a canza sunan. Daga ƙarshe fim ɗin ya fito da sunan Wasila, kuma wannan suna ya zama tamkar alamar da za ta ci gaba da biye mata har tsawon rayuwarta.

Duk da cewa, an fi saninta a matsayin jaruma, akwai wani ɓangare na rayuwarta da ya fi jan hankalin jama’a a shekaru na baya-bayan nan; rayuwar aurenta da jarumi kuma ɗan jarida, Malam Al-Amin Ciroma.

Mutane da dama daga cikin masu bibiyar Kannywood sun san su a matsayin ma’auratan da suka shafe lokaci mai tsawo tare. A cikin saƙon da ya fitar bayan rasuwarta, Al-Amin ya bayyana cewa, ya zauna da Wasila tsawon shekaru ashirin, watanni takwas da kwanaki goma sha huɗu. Wannan furuci kaɗai ya isa ya nuna tsawon tafiyar da suka yi tare kafin hanyoyinsu su rabu.

Sai dai kamar yadda yake faruwa a rayuwar mutane da yawa, ba kowane babi na aure ne yake ƙarewa cikin jin daɗi ba. Bayan rabuwar tasu, aka fara jin maganganu iri-iri daga masoya, magoya baya da masu sharhi a kafafen sada zumunta. Wasu suna kallon lamarin daga ɓangare guda, wasu kuma daga wani ɓangaren. A cewar wasu, jarumar ta furta wasu maganganu da ke nuna cewa, haƙƙin kulawa da ‘ya’yanta ya koma kanta bayan rabuwar aurenta da mijinta. 

Lokacin da aka sanar da rasuwar Wasila, mutane da dama sun yi tsammanin za a mayar da hankali ne kan addu’a da tuna kyawawan ayyukanta. 

Sai dai ba da jimawa ba, tsofaffin muhawarori suka fara dawowa. An sake tayar da batun zamanta da Al-Amin. An sake koma wa baya ana nazarin abin da ya faru a rayuwarsu. Wasu suka fara ɗora masa alhakin wasu abubuwan da suka shafi rayuwar aurensu, yayin da wasu kuma suka yi kira da a guji yanke hukunci kan abin da jama’a ba su san cikakken tarihinsa ba.

Wasu daga cikin masoya ko a ce mabiya sun musanya jimaminsu zuwa ga tausayawa tare da ɗora alhakin duk wani ɓacin rai na gidan aure da ta samu zuwa ga mijinta. A nan ne wasu ke bayyana tausayi ga ‘ya’yanta, wanda suka danganta da cewa, “sun rasa gatansu.”

A irin wannan yanayi ne Al-Amin ya zaɓi yin magana. A ranar bakwai da rasuwar marigayiyar, Al-Amin Ciroma ya fitar da saƙon da ya kira “Addu’ar Bakwai Na Wasila.”

A cikin saƙon, ya bayyana cewa, ya tsaya a kabarin tsohuwar matarsa yana yi mata addu’a. Ya kuma bayyana cewa, ya yafe mata duk wani abu da ya taɓa faruwa a tsakaninsu tun daga farkon zamansu har zuwa ranar da ta bar duniya.

Amma abin da ya fi jan hankali ba addu’ar ba ce kaɗai. A cikin wannan saƙo ne ya yi magana kai tsaye kan mutanen da suke ci gaba da aika masa saƙonnin suka da zargi. Ya bayyana cewa, mutane da yawa suna tsoma baki cikin abin da ba su da cikakken sani a kai. Ya kuma yi gargaɗin cewa bai kamata mutum ya zama mai bayar da shaida kan abin da bai sani ba. A ganinsa, akwai abubuwa da yawa da suka faru tsakanin shi da Wasila waɗanda ba kowa ya sani ba.

Wannan shine karo na farko da ya fito fili yana mayar da martani ga maganganun da suka biyo bayan rasuwarta.

Kafin ƙura ta lafa, sai wata wasiƙa da Al-Amin ya aike wa mambobin abin da ya kira “Kannywood Family” ta bayyana. A cikin wasiƙar, ya gode wa masu nuna alhini da kuma waɗanda suka yi ƙoƙarin tara gudunmawa, saboda rasuwar Wasila. Amma maimakon ya karɓi irin wannan tallafi, ya roƙi cewa duk abin da aka tara a yi niyyar sadaka ne ga marigayiyar.

A cikin wasiƙar ya bayyana cewa, addu’a da ayyukan alheri ne suka fi amfani ga mamaci. Ya kuma sake yin kira ga jama’a da su guji shiga cece-kuce kan zamantakewarsa da marigayiyar. Abin da ya fi ɗaukar hankali shine yadda ya maimaita cewa mutane da yawa suna magana ne a kan abubuwan da ba su da cikakken ilimi a kansu.

Me ya sa maganar Ciroma ta ja hankali?

Dalilin da ya sa saƙonnin Al-Amin suka zama abin tattaunawa shine, saboda sun zo ne a lokacin da ake ci gaba da ɗora masa laifi daga wasu ɓangarori. Maimakon ya shiga fallasa tarihin zamansu ko ya fara mayar da martani ga kowane zargi ɗaya bayan ɗaya, ya karkata maganarsa zuwa abubuwa uku: addu’a, gafara da kuma kira ga mutane su ji tsoron Allah wajen yanke hukunci. Wannan ya sa wasu ke ganin yana ƙoƙarin kare mutuncinsa cikin hikima, don ya kare martabar zamantakewarsu da kuma ’ya’yansu da mariogayiyar, yayin da wasu kuma ke ganin har yanzu akwai tambayoyi da ba a samu amsoshinsu ba.

Ko a wane matsayi mutum yake a kai cikin wannan muhawara, abu ɗaya da ba a musanta shi shine: mutuwar Wasila ta sake buɗe wata tattaunawa da ta daɗe tana rayuwa a cikin zukatan mutane.

Sai dai kamar yadda Al-Amin ya yi nuni a saƙonninsa, akwai bambanci tsakanin abin da jama’a suke zato da kuma abin da ya faru a zahiri tsakanin mutane biyu da suka shafe fiye da shekaru ashirin suna rayuwa tare.

Wataƙila wannan ne babban darasin da ke cikin wannan lamari, domin sau da yawa, bayan mutuwar mutum, mutane kan yi saurin zama alƙalai. Su yanke hukunci, su rarraba gaskiya da ƙarya, su ware mai laifi da wanda ba shi da laifi. Amma gaskiyar wasu labarai tana binne ne tare da masu su, ko kuma tana zaune ne a cikin gidajen da ba a taɓa shiga ba.

A yau Wasila ba ta nan, domin ta yi magana. Al-Amin kuma ya zaɓi yin addu’a maimakon shiga doguwar gardama. Abin da ya rage wa jama’a shine abin da ya kamata ya rage wa kowane mai hankali idan mutuwa ta shiga tsakanin mutane: addu’a, tausayi da kuma nisantar hukunci kan abin da ba a san cikakken tarihinsa ba, domin a ƙarshe, kamar yadda masu hikima kan faɗa, kabari kan fi kowace kotu bayyana ƙarancin ilimin da mutane suke da shi kan rayuwar wasu.

By ukarofi