Kiwo: Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa mata da matasa 37,000

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana shirinta na ƙarfafa mata da matasa 37,000 ta hanyar wani sabon shiri a ɓangaren kiwo, domin bunƙasa masana’antar madara ta ƙasa da kuma ƙara yawan samar da madara a cikin gida.

Ministan Raya Harkokin Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Ranar Madara ta Duniya ta 2026 da aka gudanar bayan wani gangamin wayar da kai a Abuja.

Ministan, wanda Babban Mataimakinsa na Musamman, Farfesa Eustace Iyayi ya wakilta, ya ce gwamnati na ƙara ƙarfafa manufofin da ke bai wa mata dama tare da faɗaɗa damar da mata da matasa za su samu a dukkan sassan harkar samar da madara.

Ya bayyana cewa, sabon shirin da ake kira Shirin ƙarfafa Mata Da Matasa A Fannin Kiwo (Women and Youth in Livestock Empowerment Initiative) zai mayar da hankali kan samar da madara, sarrafa ta, tallata ta da kuma samar da damammakin kasuwancin noma.

A cewarsa, shirin wanda a halin yanzu ake tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kansa, zai samar wa waɗanda za su amfana da horo da koyar da sana’o’i, tallafin kasuwanci, damar samun kuɗaɗen jari, musayar fasahohi da kuma haɗa su da kasuwanni.

Ministan ya kuma bayyana cewa Tsarin Aiwatar da Manufofin ƙasa Kan Samar da Madara (National Dairy Policy Implementation Framework), wanda ake sa ran ƙaddamar da shi a ranar 1 ga Yuni, zai zama taswirar da za ta jagoranci aiwatar da manufofin ƙasa kan bunƙasa harkar madara.

Ya ƙara da cewa, gwamnati na ƙara zuba jari ta ƙarƙashin Dabarar ƙasa Ta Hanzarta Bunƙasar Kiwo (NL-GAS), musamman a fannoni kamar samar da abincin dabbobi, kula da lafiyar dabbobi, cibiyoyin samar da madara, wuraren tattara madara, tsarin adana kayayyaki masu sanyi da kuma hanyoyin kiwo masu la’akari da sauyin yanayi.

Tun da farko, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Raya Harkokin Dabbobi, Dakta Chinyere Ijeoma Akujobi, wadda Daraktan Raya Dabbobi Masu Tauna Ciyawa Da Marasa Taunawa, Victor Egbon, ya wakilta, ta ce taken Ranar Madara ta Duniya ta bana mai taken “Girmama Mata Manoma” na nuna muhimmiyar gudunmawar da mata ke bayarwa wajen samar da madara, tabbatar da wadatar abinci da kuma bunƙasa tattalin arzikin karkara.

Taron ya samu halartar wakilan hukumomin gwamnati, abokan hulɗar raya ƙasa da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a fannin noma da kiwo.

By ukarofi