Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Cibiyar Bunƙasa Masana’antu Masu Zaman Kansu (CPPE) ta bayyana cewa cire tallafin man fetur da kuma haɗa tsarin farashin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje su ne manyan sauye-sauyen tattalin arziki da suka taka muhimmiyar rawa wajen farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wata sanarwa mai taken “Shekaru Uku Na Gwamnatin Tinubu: Daga Daidaita Tattalin Arziki Zuwa Wadata Ga Kowa”, Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na CPPE, Muda Yusuf, ya ce waɗannan tsare-tsare sun taimaka wajen fitar da tattalin arzikin ƙasar daga mawuyacin halin rashin daidaito tare da shimfiɗa harsashin ci gaba mai ɗorewa.
A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta gaji tattalin arzikin da ke fama da matsanancin gibin kuɗaɗen gwamnati, matsalolin musayar kuɗi da sauran barazanar da ke iya raunana tattalin arzikin ƙasa, lamarin da ya sa dole aka ɗauki tsauraran matakan gyara domin dawo da daidaito.
Ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da kuma daidaita farashin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje sun kasance ginshiƙan manufofin gwamnatin na daidaita tattalin arziki, duk da wahalhalun da jama’a suka fuskanta a farkon aiwatar da su.
“Ko da yake an fuskanci ƙalubale a farkon aiwatar da waɗannan sauye-sauye, akwai ƙarin hujjojin da ke nuna cewa sun taimaka wajen samar da daidaito a tattalin arzikin ƙasa,” inji Yusuf.
Ya yi nuni da yadda ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ta Nijeriya ke ƙara ƙarfi, inda ya ce tana daf da kaiwa dala biliyan 50, tare da ci gaba da samun rarar cinikayya da ƙaruwa amincewar masu zuba jari da kuma raguwar sauyin farashin canjin kuɗi tun daga shekarar 2025.
Muda Yusuf ya kuma bayyana cewa bunƙasar tace man fetur a cikin gida, musamman ta hannun matatar Dangote, na daga cikin manyan abubuwan da suka taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.
A cewarsa, ƙarin tace man fetur a gida ya rage dogaro da shigo da albarkatun man fetur daga ƙasashen waje, ya taimaka wajen adana kuɗaɗen musayar waje, ya ƙarfafa tsaron makamashi tare da taimakawa wajen daidaita darajar naira.
Ya ce, “Tattalin arzikin da ke samar da mafi yawan abubuwan da yake amfani da su a cikin gida ya fi ƙarfi kuma ya fi juriyar fuskantar matsaloli.”
Duk da ci gaban da aka samu, Yusuf ya jaddada cewa dole ne gwamnati ta tabbatar da cewa nasarorin da aka samu wajen daidaita tattalin arziki sun kai ga inganta rayuwar talakawa kai tsaye.
Ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki, raguwar ƙarfin sayen jama’a da kuma rashin ƙarfin gwiwar gidaje har yanzu suna daga cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta.
A cewarsa, mataki na gaba shi ne mayar da nasarorin da aka samu zuwa ci gaban da zai amfani kowa ta hanyar samar da ayyukan yi, ƙara kuɗaɗen shiga, rage talauci da kuma inganta rayuwar ’yan Nijeriya.
Shugaban CPPE ya kuma bayyana rashin tsaro a matsayin babban cikas ga farfaɗowar tattalin arziki, musamman a fannin noma.
Ya ce, hare-haren da ake kai wa al’ummomin manoma na ci gaba da kawo cikas ga samar da abinci, lamarin da ke ƙara haddasa tashin farashin kayan masarufi.
Ya jaddada cewa inganta tsaro a yankunan karkara zai taimaka wajen bunƙasa noma da tabbatar da wadatar abinci a ƙasar.
Muda Yusuf ya kuma nuna damuwa kan yadda bashin Nijeriya ke ci gaba da ƙaruwa, inda ya ce ya kai naira tiriliyan 159.3 zuwa watan Disamban 2025.
Ya bayyana cewa raguwar darajar naira ta sa bashin ƙasashen waje ya ƙaru idan aka lissafa shi da kuɗin Nijeriya. Haka kuma, sauya bashin Ways and Means na Naira tiriliyan 23 zuwa tsarin bashi na hukuma ya taimaka wajen ƙara girman bashin gwamnati.
Sai dai ya ce sauye-sauyen da ake yi a tsarin haraji na iya taimakawa wajen ƙara kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma tabbatar da ɗorewar harkokin kuɗi a matsakaicin lokaci.
