An ci tarar Atletico Madrid bayan hatsaniyar da aka samu a wasanta da Real Madrid

Spread the love

Hukumar Kula da ƙwallon ƙafar ƙasar Sifaniya ta ladabtar da ƙungiyar Atletico Madrid, bayan da magoya bayanta sukai ta jefo abubuwa cikin fili a lokacin wasan hamayyar da suka yi da Real Madrid a ƙarshen mako.

Mai tsaron ragar Madrid Thibaut Courtois ne ya yi ƙorafin cewa magoya bayan ƙungiyar da ke zaune a bayan ragarsa, na jefo abubuwa cikin fili, lamarin da ya sa aka yi amfani da amsakuwa wajen buƙutar su bari, amma kuma suka yi burus da hakan, dole sai da aka dakatar da wasan na tsawon minti 20 da wasu daƙiƙu.

Kwamitin ladabtarwa na hukumar ya yanke hukuncin cewa ƙungiyar za ta rufe yankin da magoya bayanta da suka tada hatsaniya a filin wasanta na Metropolitano suke zaune na tsawon wasanni uku, sannan kuma za ta biya tarar Euro dubu 45.

Tun kafin ɗaukar wannan mataki dai, hukumomin ƙungiyar na Atletico Madrid suka ce sun gano magoyin bayan su da ya haifar da matsalar tare kuma da hanashi shiga filin wasanta.

A ƙarshen wasan na hamayyan an tashi 1-1 ne, domin ana daf da tashi daga wasanne dai Angel Correa ɗan wasan Atletico Madrid ya farke musu kwallon da Eder Militao ya jefa musu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

By ukarofi