Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Lille da ke Faransa, ta kawo ƙarshen wasanni 37 da Real Madrid ta yi ba tare da rashin nasara ba, lamarin da ya sa mai horas da ƙungiyar Carlo Ancelotti, ya ce masu sukarsu game da rashin nasarar da ƙungiyar ta yi a gasar zakarun Turai sun cancanci su yi.
Ancelotti ya bayyana hakan ne a bayan tashi daga wasan da Lilli ta samu nasara a kansu da ci ɗaya mai ban haushi.
Batu na gaskiya dole mu yarda cewa bamu buga wasa yadda ya kamata, don haka sukar da ake mana abu ne da ya kamata.
Tun kafin aje hutun rabin lokaci ne dai Jonathan Daɓid ya jefa ƙwallo a ragar Real Madrid a bugun daga kai sai mai tsaron gidan da suka samu, wanda ya kawo ƙarshen wasanni 37 da ƙungiyar ta yi ba tare da rashin nasara ba.
ɗan wasan gaba na ƙungiyar Lille Jonathan Daɓid lokacin da ya ke murnar jefa ƙwallo a ragar Real Madrid.
Haka nan kuma wannan ce rashin nasara ta farko da ƙungiyar ta yi a gasar zakarun Turai, tun bayan wacce ta yi a hannun Manchester City a wasan kusa dana ƙarshe da suka yi a watan Mayun shekarar bara.
Madrid dai ta samu nasara a wasan farko a wannan gasa da tayi a gasar Turai, inda ta doke VfB Stuttgart da ci 3-1, sai dai kuma ta bi sahun manyan ƙungiyoyin turai irinsu PSG da Bayern Munich da Atletico Madrid da ma Barcelona da makwanni biyu da suka gabata itama ta yi rashin nasara a wannan gasa.
