Mourinho ya koka da na’urar VAR

Spread the love

An bai wa Jose Mourinho katin gargaɗi ranar Asabar, bayan da ya yi ƙorafi kan hukuncin ɓAR a karawa da Fernabahce ta doke Antalyaspor.

Mourinho ya yi ƙorafi kan ƙwallon da suka ci aka soke da cewar an yi satar gida, sai kocin ya ɗauki komfuta ya ɗora a kan kamara da nufin nuna wani hoto cewar an yi kuskuren hukuncin.

Tsohon kocin Manchester United da Chelsea da kuma Real Madrid ya sanar da manema labarai cewar Edin Dzeko bai yi satar gida ba.

”Mu a wajenmu ƙwallo mai ƙyau aka ci,” kamar yadda Mourinho ya sanar bayan tashi daga wasan da suka doke Antalyaspor 2-0 a gasar Turkiya wato Turkish Super Lig.

“Ina son aikin ɓAR. Ina ƙaunar aikin da ɓAR za ta gudanar da zai saukakawa alƙalin ƙwallon ƙafa yanke hukunci na adalci.”

Cikin watan Afirilu, shugaban Fenerbahce, Ali Koc ya zargi mahukuntan gasar Turkiya da yi wa ƙungiyarsa rashin adalci daga baya aka yi hayar masu kula da VAR daga waje zuwa ƙarshen kakar 2023-24.

A bara ne Fernabahce ta kare a mataki na biyu a kan teburin babbar gasar tamaula ta Turkiya da tazarar maki uku tsakani da mai kofin Galatasaray.

Ranar Alhamis Mourinho zai ziyarci FC Twente a Europa League.

By ukarofi