An cinna gobara a fadar Sarki Sanusi

Spread the love

Daga FAROUK ABBAS

Wani rahoto daga jihar Kano ya ce gobara ta kama a fadar Sarki Sanusi da ke Gidan Rumfa wanda ake zargin waɗansu da ba’a san ko su waye ba ne suka cinna ta, inda a nan ne Sarkin ya ke.

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na daren Juma’a, a Ƙofar Kudu wanda a nan ne Sarkin ya ke zaman kotu duk ranar Litinin.

Wani mutum da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce suna zargin an buɗe mukullin ƙofar ne da ƙarfi sai kuma aka shiga ciki aka cinna wuta kana sai aka sake kulle kofar wanda ya yi sanadiyar ƙone kujerar Sarauta, fankokin busa sanyi da wasu abubuwa masu tsada.

Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce bai san da batun ba kuma babu wani kira kan haka a dukkan ofishinsu.

Sai dai a wani ɓangaren, shugaban ma’aikatan Sarkin, Munir Sanusi Bayero (Dan Buram) ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce babu batun rasa rai ko raunuka, sannan damejin da aka samu taƙaitattu ne.

Ya ƙara da cewa, suna cigaba da bai wa fadar duk wasu matakan kariya da waɗanda ke cikin ta, sannan suna gudanar da bincike game da musabbabin abin ya haifar da gobarar domin kiyaye aukuwar irin haka a gaba.

By Babaji