An dakatar da Cynthia ta Nijeriya daga gasar Olympics bisa gwajin ƙwayoyi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

An dakatar da ƴar wasan ‘boxing’ ta Nijeriya, Cynthia Ogunsemilore daga shiga gasar Olympics sakamakon gwajin ƙwayoyi da aka yi mata a ranar Asabar a yayin da ake cigaba da shirin wasanta na farko.

Hukumar gwajin ƙwayoyi ta ƙasa-da-ƙasa, ta ce bayan gwajin Cynthia an tabbatar cewa ta na shan maganin ‘furosemide wanda yana daga cikin ababan da hukumar ta haramta wa ƴan wasa.

Shafin ATI ya wallafa cewa, a halin yanzu an dakatar da ita har sai an warwara matsalar kamar yadda ya ke a cikin dokokin kwamitin gasar.

Sannan, hakan ya nuna cewa Cynthia ba za ta shiga gasar ko lamuran horarwa ko kowane irin aiki a Olympics ɗin shekarar nan da ake yi a Farisa ba.

ITA ya ce, ƴar wasan ta na da damar shigar da ƙara kotu gabanin fara wasan.

Haka nan, matakin ya ƙara rage adadin masu wakiltar Nijeriya a ɓangaren boxing na gasar inda Adam Olaure ne ƙadai wanda ake sa ran zai samo nasara wa Nijeriya a halin yanzu.

By Babaji