Nijeriya ta tsaurara tsaro a iyakokin ƙasa gudun shigowar ɓatagari lokacin zanga-zanga

Spread the love

Gwamnatin tarayya ta tsaurara tsaro kan iyakokinta domin hana shigowar ɓatagari a yayin zanga-zangar matsin rayuwa da aka shirya yi 1 ga watan Agusta 2024

Shugaban hukumar shige da fice Kemi Nandap ta bada umarnin duk ma’aikatan su da su ƙara sanya ido domin gujewa shigowar ɓata gari.

Kuma ta dakatar da ma’aikatan hukumar daga tafiya hutu har sai an gama zanga-zangar. Ta yi kira kuma da su zama yan ƙasa nagari masu kishin ci gaban Nijeriya.

By ukarofi