Facebook sun goge shafin Mawaƙi Rarara biyo bayan rubdugun ƙorafi

Spread the love

Facebook sun goge shafin sanannen mawaƙin siyasan nan Dauda Kahutu Rarara biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da mutane su ka shigar dalilin yin wa Shugaba Bola Tinubu waƙa.

Hakan ya biyo bayan wata waƙa da ya saki a shafin na shi, wanda a cikin ta yake yabon shugaban Tinubu da cewa yayi maganin yunwa, talauci da kuma tsaro.

Wannan waƙar ya saketa a lokacin da ‘yan Nijeriya ke fama da matsalolin hauhawar farashin kayan abinci, rashin tsaro da matsanancin talauci. Wannan shi ya tunzura mutane su kai ta kai ƙarar shafin nasa ga Facebook.

Mawaƙin in ba mu manta ba, satin da ya gabata mahaifiyar shi ta samu ‘yanci bayan shafe kwanaki a hannun masu garkuwa da mutane.

By ukarofi