Dalilan da su ka dawo da layukan man fetur a Abuja da Legas – NNPCL

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ce tseko da ake samu daga wuraren jido man fetur su suka haifar da wahalarsa a Abuja da Legas.

Wata sanarwa da Jami’in yaɗa labara NNPL, Olufemi Soneye ya fitar a ranar Asabar, ta ce kamfanin na ƙoƙari wajen shawo kan matsalar, kamar yadda ‘Blueprint’ ta ruwaito.

Ya ce, suna cigaba da aiki tuƙuru da masu-ruwa-da-tsaki domin ganin an warware matsalolin da ke haifar da layukan.

Soneye, ya ƙara da cewa su na fatan nan ba da jimawa ba za a dawo sayen man yadda aka saba a wuraren da lamarin ya shafa.

By Babaji