
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƴar Shugaba Tinubu, Folshade Tinubu-Ojo ta caccaki zanga-zangar tsadar rayuwa da aka shirya yi a Nijeriya, tana mai cewa hakan wa ƙoƙarin da mahaifinta ke yi wa ƙasar ya yi wuri.
Folshade wacce ita ce babbar ‘Iyaloja’ ta Jihar Legas ta faɗi hakan ne a lokacin da take ganawa da taron ƴan kasuwa cikin wata ɗaukar bidiyo a ranar Lahadi a Jihar Legas.
A lokacin da ta ke magana da mata ƴan kasuwa ta harshen Yarbanci, Folshade ta yi kira gare su da su gargaɗi ƴaƴansu game da haɗurran zanga-zanga, ta na mai bada misali da waɗanda aka yi a baya da damejin da su ka haifar kamar na lokacin ‘EndSars’.
Ta kuma yi tsokaci game da gwamnatin Legas inda ta ce ana samun cigaba mai amfani don haka akwai buƙatar al’umma su ba ta goyon baya tare da kaucewa zanga-zanga.
Tinubu-Ojo ta ƙara da cewa, Gwamnatin Tarayya da mahaifinta ke jagoranta, ta na buƙatar a ba ta lokaci kafin a soke ta.
Wannan shi ne karo na biyu da Folshade ke kira ga ƴan Nijeriya su kasance masu haƙuri game da shugabancin mahaifinta tun da ta yi irin hakan a wata Fabrairu.
Matasa da dama na shirin zanga-zangar wacce za a fara daga ranar 1 ga watan Agusta, duk da cewa gwamnatin ta yi ta ƙoƙarin dakatar da aukuwar lamarin tun a satittikan da su ka gabata.
Masu zanga-zangar su na buƙatar gwamnati ta shawo kan matsalolin hauhawar farashi da tsadar rayuwa gami da sauran al’amuran da su ka haddasa wahalhalun rayuwa a faɗin ƙasar.
