Tinubu ya cigaba da aikin titin Abuja zuwa Kano da Buhari bai kammala ba – Ministan Ayyuka

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta koma aikin tItin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano mai tsawon kilomita 375.9.

Ministan ayyuka, Engr. David Umahi, ya bayyana hakan ne a jiya a yayin ƙaddamar da aikin aikin titin mai tsawon kilomita 38 ga rukunin kamfanin Dangote.

Umahi a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Barista Orji Uchenna ya fitar, ya buƙaci kamfanoni uku da ke kula da sassan uku da su nuna cikakkiyar sadaukarwa ga kammala aikin.

Ya yi nuni da cewa ma’aikatar za ta duba buƙatar sake duba kuɗi domin daƙile illolin hauhawar farashin kayayyaki.

Ya ce, “Kashi na farko shi ne kilomita 38 da biyu, wato kilomita 76. An fara aikin ne a yau, tare da kayan aikin a ƙasa, sannan kuma za su fara sanya shingen siminti mai ƙarfi.”

Umahi ya kuma ƙaddamar da shirin gwamnatin tarayya na ‘Operation Free Our Roads’ da nufin tabbatar da cewa dukkan hanyoyin gwamnatin tarayya da ake gyarawa sun kasance masu ƙarko daga wannan damina.

Ya jaddada buƙatar injiniyoyin ma’aikatar su ɗauki aikin da muhimmanci, ciki har da hukumar FERMA.

By ukarofi