Yaran Nijeriya sun roƙi Tinubu ya dakatar da zanga-zangar tsadar rayuwa

Spread the love

Daga KAHLID IDRIS DOYA a Bauchi

Ƙungiyar yaran Nijeriya, NCCF sun koka wa Shugaba Tinubu kan cewa ya ɗauki matakan da demokradiyya ta bada dama wajen dakatar da zanga-zangar gama-gari da ke tafe a watan Agusta.

Jagorar ƙungiyar, A’isha Hassan Saraki wacce ɗaliba ce makarantar ‘Sunshine International’, ta gana da manema labarai a ranar Asabar inda ta ce a matsayinsu na jikokin Tinubu, su na kira gare shi da ya bi hanyoyin da doka ta amince da su wajen magance matsalolin Nijeriya.

A’isha mai shekaru 8, ta ce a madadin iyayensu da ma ƙasa baki ɗaya su na roƙo da a bi hanyoyin da su ka dace wajen daidaita al’amura domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

Wata ɗalibar mai suna Precious Fashola daga Jihar Ogun, ta roƙi ƴan zanga-zangar su sake nazari kan shirye-shiryensu, ta na mai kira ga Tinubu da ya shirya tattaunawa da su.

Daga ƙarshe, yaran ƙungiyar sun kuma buƙaci al’ummar Nijeriya su kasance masu addu’o’i da fatan matsalolin da ake fama dasu su zama tarihi.

By Babaji