Ƙungiyar iyaye mata ta roƙi masu shirin zanga-zanga su yi haƙuri

Spread the love

Wata ƙungiyar iyaye mata masu addu’a, sun yi kira da ‘yan Nijeriya da kar suyi zanga-zanga domin wanzar da zaman lafiya da cigaban ƙasa.

Shugabar ƙungiyar ta ƙasa Rev. Dr Lois Angula ce ta faɗi haka a Abuja yayin ganawa da ‘yan jarida. Ta ce, tabbas ‘yan Nijeriya na cikin matsin rayuwa, amma zanga-zanga ba ita ba ce za ta kawo sauƙi ba.

A cewar ta, zanga-zangar ka iya rikiɗewa ta zama tashin hankali sosai. A na ta faɗin, addu’a ya dace yanzu ba zanga-zanga ba.

Ta cigaba da cewa, shugaba Tinubu addu’a ya ke buƙata yanzu ba zanga-zanga ba. Ta bada misali da irin abubuwan da suka faru lokacin zanga-zangar #ENDSARS. In ji ta, ta ce mun ga yadda a ka samu tashin hankali da asarar dukiyoyi da rayuka. Ba mu san haka ya sake faruwa.

A matsayin mu na masu addu’a, zamu cigaba da yi ma ƙasa addu’a, da kuma wayar da kan ƴan ƙasa a kan muhimmancin addu’a.

By ukarofi