An dangata wasu tsoffin gwamnonin Nijeriya da dukiyar sata a Birtaniya

Daga WAKILINMU

Wani sabon rahoto da aka fitar kwannan ya nuna yadda wasu tsofoffin gwamnonin Nijeriya su goma ke da alaƙa da wasu tarin haramtattun kadarori a Ƙasar Birtaniya wanda darajarsu ta kai Pan milyan £56, wato kwatankwacin Naira bilyan N30 kenan.

Rahoton kan hada-hadar haramtattun kuɗaɗe (IFF) daga Nijeriya zuwa Birtaniya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ya kuma nuna wasu kadarori 216 mallakar wasu jami’an Nijeriya su 13 da aka girke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

A cewar jaridar SaharaReporters, an gabatar da rahoton ne a wajen taron da cibiyar Human and Environmental Development Agenda tare da haɗin gwiwar Gidauniyar MacArthur suka shirya.

Sai dai rahoton ya yi shiru bai bayyana gwamnonin da lamarin ya shafa ba, haka ma bai sanar da takamammen wurin da aka gudanar da taron ba.

Dr. Gbenga Oduntan na Kent Law School a Jami’ar Kent da ke UK, shi ne ya gabatar da wannan rahoto mai taken, “Daƙile Hanyoyin Hada-hadar Kuɗaɗen Haramun na Nijeriya: Nazari Kan Dokokin Birtaniya da Daular Laraba.”

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan rahoton, Shugaban cibiyar HEDA, Olanrewaju Suraju, ya ce akwai tashin hankali matuƙa dangane da lamarin satar kuɗaɗen Nijeriya da ake ana kaiwa a ɓoye a UK da UAE.

Ya ce waɗannan ƙasashen biyu sun zama tamkar ma’adanar kuɗaɗen sata, tare da jaddada buƙatar da ke akwai na ƙalubalantar masu agazawa daga waje wajen fitar da kuɗaɗen sata daga Nijeriya.

A cewarsa, “Ya kamata mu sanya ya zama al’amari mai wahalar gaske wajen iya ci gaba da aikata manyan laifuka.”

Yana mai cewa, “ya kamata Birtaniya da Haɗaɗɗiyar Daular Laraba su kare kansu daga sharrin irin waɗannan kuɗaɗe na sata.

Ya ci gaba da cewa kuɗi sama da Dala bilyan $50 ke ɓacewa duk shekara a nahiyar Afirka, kuma Nijeriya ita ce kan gaba bisa ga sauran ƙasashen Afirka game da wannan matsalar.

Ya ce domin kawo ƙarshen wannan matsala kuwa, wajibi ne Nijeriya ta haɗa kai da ƙasashen da ake kai kuɗaɗen ana ɓoyewa don su daina bada haɗin kai wajen shigo musu da kuɗaɗen sata.