Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da aikin titin kilomita 1068 a Arewa maso yamma tare da samar da dam 68 don ƙarfafa noman rani a Arewa.
Bayan shekaru 40 da wofantar da aikin babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cigaba da aikin don sauƙaƙa sufiri da kawo ƙarshen ƙalubalen da matafiya ke fuskanta tsakanin yankin Kudu maso Yamma da kuma Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Al’ummar Arewa maso Yamma sun bayyana farin cikin su bisa wannan aiki. Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya bayyana farin cikin sa a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da wannan katafaren aiki a garin Gulumbe dake ƙaramar hukumar Birnin Kebbi a jihar Kebbi.
A cikin jawabin sa, ya bayyana cewa ba iya mutanen Arewa maso Yamma ba, gaba ɗaya al’ummar Nijeriya na cikin farin ciki da wannan aiki.
“Muna Godiya ga Allah da ya ba ka (Shugaba Tinubu) yawan rai tare da sauke nauyin da ya rataya a wuyan ka a matsayin ka na shugaban ƙasa, kayi alƙawarin zama shugaban ƙasa ga kowa a ƙasar nan ba tare da nuna banbanci ba, tabbas munyi farin ciki da ka cika wannan alƙawari”
“Ka soma gudanar da katafaren aikin da ba a taɓa irin sa ba a tarihin ƙasar nan, ina mai farin cikin tabbatar da cewa Shugaba Tinubu bai bawa ‘yan Nijeriya kunya ba”
“Ina amfani da wannan dama na ƙara gode ma Shugaban Ƙasa, majalisar zartarwa ta ƙasa da kuma Majalisar Dattijai da ta wakilai bisa ƙoƙarin su na tabbatar da fara wannan aikin.”
Ya kuma taya Jihar Kebbi murna da ta zama jihar da ta fara amfanar kaso mai tsoka na wannan aiki tare da tabbatar da cewa ba za a samu koma baya ba wajen gudanar da aikin.
Aikin wanda ya kai tsawon Kilomita 1068 ya samo asali ne tun 1980s a zamanin Shehu Shagari yana shugaban ƙasa, aka wofintar dashi har tsawon shekaru 40 sai bayan zuwan shugaba Bola Tinubu.
A nasa jawabin, ministan ayyyka David Umahi ya bayyana wannan aikin a matsayin gagarumin aikin da zai inganta walwalar sufuri da kuma bunƙasa abubuwan cigaba a yankin.
Ya bayyana cewa sashi na farko na aikin ya haɗa da samar da Damadamai 68 don inganta noman rani.
“Aikin ba wai iya gundarin samar da hanya bane, hannun jari ne da ke da riba mai girma. Hanyar tana da damadamai guda 68 da za su bunƙasa noman rani a yankin. Sannan za a samu wadatacciyar iska da za a yi amfani da ita a matsayin makamashi” inji shi.
A nashi ɓangaren, ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na tattalin arziki ya ƙara da cewa, shugaba Tinubu a lokacin yaƙin neman zaɓen sa bai yi alƙawarin yin wannan aiki ba, amma yayi alƙawarin zama shugaban ƙasa ga kowa babu wariya, kuma a yau sun tabbatar da hakan.
A nashi ɓangaren, Adamu Aliero wanda shine shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattijai kuma tsohon Gwamnan Jihar Kebbi ya yaba da wannan aikin da kuma salon mulkin Gwamnan Jihar Kebbi Idris.
“Ni ɗan jam’iyyar PDP ne, kuma gwamna Idris ɗan jam’iyyar APC, to amma dole yaba masa. Gwamna Idris ya kawo babban cigaba Jihar Kebbi”
Haka zalika shima Sarkin Gwandu da shugaban majalisar Sarakuna, Alhaji muhammadu Iliyasu-Bashar (Mai Ritaya) ya bayyana godiyar sa ga gwamnatin tarayya bisa wannan cigaba da ya zo Jihar Kebbi da ma Arewacin Najeriya baki ɗaya.