Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
CBEX wani tsarin zuba jari ne ta intanet da ke ninka wa mutane kuɗin da suka zuba cikin wata guda, suna kuma samun ƙarin kuɗi idan suka kawo wani cikin harkar.
’Yan Nijeriya da dama sun yi ta nuna ɓacin-rai a kafofin sada zumunta bayan asara da suka tafka a wannan tsari na CBEX.
Waɗanda suka zuba jari a tsarin sun ce sun aasa cire kuɗaɗensu na tsawon kwanaki, inda lokacin da suka zo cire kuɗin suka samu babu ko sisi a asusansu.
CBEɗ dai wani tsarin zuba jari ne na dijital wanda yake ninka wa masu zuba jari da kashi 100 cikin wata guda.
Masu zuba jarin suna kuma samun ƙarin kuɗi idan suka kawo wani cikin harkar.
CBEX ɗin wanda ya kasance yana hada-hadar kuɗin kirifto, ya fara aiki a Nijeriya a shekara da ta gabata.
Lamarin ya kai ga wasu fusatattun matasa afka wa ofishin CBEX a Ibadan, inda suka wawushe kayayyaki a ofishin.
Tun da farko dai, Hukumar da ke Kula da Hannayen Jari ta Nujeriya (SEC), ta gargaɗi ‘yan Nijeriya kan mu’amala da kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet da ba a yi wa rajista ba.
Ta ce, babban laifi ne yin hulɗa da irin waɗannan kamfanoni.
A ɗaya ɓangaren, masu zanga-zanga sun farfasa ofishin CBEɗ na birnin Ibadan a jihar Oyo da ke kudancin Nijeriya.
A ranar Talata ne masu zuba jari a kamfanin da ke karɓar kuɗaɗen mutane don kasuwanci suka riƙa bayyana damuwa cewa an hana su taɓa kuɗaɗensu daga kan manhajar.
Rahoton ya ce zanga-zangar ta yi ƙamari lokacin da mutane suka lura an kwashe duka kuɗaɗen da suka zuba a asusunsu na manhajar.
Wasu rahotonni sun ce an lakaɗa wa wasu ma’aikatan kamfanin duka lokacin da masu zanga-zangar suka kutsa ginin.
