Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mambobin rusasshiyar jam’iyyar CPC ta tsohon Shugaban ƙasa, Muhammad Buhari, sun jaddada goyon bayansu ga jam’iyyar APC da kuma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a siyasance.
Cikin wata sanarwa da suka fitar ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura sun yi watsi tare da musanta zargin rashin jin daɗin APC da kuma rahotannin da ke cewa za su fice daga jam’iyyar.
“Muna jaddada cewa ba mu fita ba ko niyyar ficewa daga APC,” a cewar sanarwar mambobin tsohuwar CPC da suka ƙunshi har da ministocin gwamnatin Buhari.
Sai dai duk da sun jaddada goyon bayansu ga shugaba Bola Ahmed Tinubu amma ‘yan tsohuwar CPC sun yi kira ga shugabancin APC ya yi tafiya da dukkanin ɓangarorin jam’iyyar a kowane mataki.
Baya ga Al-Makura, ‘yan jam’iyyar CPC da suka sanya hannu kan sanarwar sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari; Mallam Adamu Adamu, Sanata Ibrahim Musa, Sanata Mustafa Salihu, Hon. Farouk Adamu Aliyu, Hon. Almajiri Geidam, Arc. Waziri Bulama, Dr. Nasiru Ladan Argungu, Dr. Dominic Alancha, Hon. Ayuba Balami, Mr. Osita Okechukwu, da Cif Okoi Obono-Obla.
Sauran su ne Hon. Lucy Ajayi, Captain Bala Jibrin, Hon. Uche Ufearoh, Alh. Yusuf Salihu, Hon. Abubakar Maikudi, Engr. Mutallib Badmus, Alh. Mohammed Ahmed Datti, Hon. Muhammed Etsu, Cif Jerry Johnson, da Alh. Alkali Ajikolo.
Idan za a iya tunawa cewa jam’iyyun CPC, Action Congress of Nigeria (ACN), All Nigeria Peoples Party (ANPP), wani ɓangare na jam’iyyar All Progressiɓes Grand Alliance (APGA) da kuma wani ɓangare na jam’iyyar PDP mai suna nPDP sun haɗe suka kafa APC a shekarar 2013.
Alamu na nuna cewa wasu ‘ya’yan jam’iyyar CPC a jam’iyyar APC sun kammala shirin ficewa daga jam’iyyar bisa zargin rashin yi musu adalci.
Amma ƙungiyar da Al-Makura ke jagoranta ta ce, “muna bayyana cewa ba mu fita daga APC ba, kuma ba mu da niyyar ficewa, jam’iyyar CPC ta kasance ɗaya daga cikin ginshiƙan jam’iyyar APC, kuma mun tsaya tsayin daka wajen tabbatar da jam’iyyar da manufofinta na ci gaba.
