Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya yi kira da a gaggauta haɗa ƙarfi da ƙarfe domin magance matsalar sauyin yanayi wanda ke shafar noma a faɗin Afirka.
Ya yi wannan kalamai ne a yayin taro karo na 6 na ƙara wa juna sani kan noman rani da samar hanyar ruwa wanda aka yi a Abuja a ranar Litinin.
Zulum ya ce Afrika na cikin wani mawuyacin hali inda ya jaddada buƙatar samar da wani tsari na baiɗaya da dabarun samar da abinci.
“A faɗin yankin Afirka da sahara, kaso 65% na gonaki na dogara ne da ruwan sama wanda a yanzu ba ya zuwa kamar da. Yanayin damuna na wucewa nan da nan a yayin da rani ke ƙara tsayi, ga kuma ambaliyar ruwa da ke ƙara tsananta,” ya faɗa.
A yayin da yake buga misali da rahoton Bankin Duniya kan sauyin yanayi na shekarar 2023, ya ce an samu raguwar saukar ruwan sama da kaso 20-30 cikin ɗari a yankin Sahel a ‘yan shekarun bayanan nan.
“Sakamakon hakan shi ne za a samu raguwar abincin da ake nomawa da kaso 50% daga yanzu zuwa 2030 idan aka cigaba da fuskantar matsalar sauyin yanayi a cewa hukumar bibiyar noma da samar da abinci (FAO).”
“Wannan ba kawai ƙiyasi ba ne. Wannan abu ne da ya shafi barazana da muke fuskanta ta ɓangaren abinci da lafiyar al’umma da kuma makomai miliyoyin mutane.”
“Duk da irin cewa muna fitar da ƙasa da kaso 4% na ɗaukacin ɗumamar yanayi, Afirka na cigaba da fuskantar sakamakon sauyin yanayi.”
“Babban misali shi ne tafkin Chadi wanda ya rasa sama da kaso 90% na yawan ruwan da ake samu tun daga shekarar 1960. Noman rani ba zaɓi ba ne, tilas ne,” a cewar Zulum.
Ya jaddada buƙatar a sauya dabarar dogaro da ruwan sama wajen noma zuwa dabarun magance sauyin yanayi domin yin noman rani.
“Dabarun zamani kamata ya zama na kowa da kowa ne maimakon na wasu ‘yan ƙalilan. Matakan da za mu ɗauka dole ne su tallafa wa ƙananan manoma musammann mata da matasa waɗanda su ne ƙashin bayan noma a karkara.”
Gwamnan ya ce, jihar Borno ta fara kafa harsashin noma daga tushe da sabunta tsarin noman rani mai ɗorewa a jihar.
Ya buƙaci a samar da yunƙuri da zai hada kowa da kowa a maimakon wasu jihohi ko ƙasashe.
“Wannan lokaci ne na tafiya tare a Afirka. Samar da dabaru na baiɗaya ga noman rani da kula da sha’anin ruwa wanda ke buƙatar samar da dokoki da zuba jari da shigo da al’umma ciki,” ya faɗa.
Ya yi kira ga abokan samar da haɗin guiwa da su yi aiki da ƙasashen Afirka ta hanyar samar da mafuta daidai da matsalolin da ake fama da su.
“Ba ma buƙatar dagaro da wasu, abin da muke buƙata shi ne haɗin guiwa mai cike da hikima. Samar da tsarin da zai magance tasirin sauyin yanayi da dawo da ƙimar al’ummarmu.”
Wannan taro dai ana cigaba da yinsa a Abuja har zuwa 17 ga watan Afirilu kuma zai ƙunshi tattaunawa tsakanin masana harkar doka da dabaru na musamman da kai ziyara wuraren da ake noman rani a faɗin Najeriya.
