Sarkin Fika ya naɗa wa fitattun mutane shida sarautun gargajiya 

Spread the love

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMMAD 

Mai Martaba Sarkin Fika, Aljaji Dr Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa ya naɗa fitattun mutane shida da sarautun gargajiya.

Waɗanda aka naɗa sune: Air Marshal Muhammad Dikko Umar (murabus) a matsayin Ja’idinawa Fika, (Sarkin Fulani Ja’idinawa), Air vice Marshal Alkali Muhammad Mamu (murabus) a matsayin Barden Fika, DIG Bala Ciroma (murabus) a matsayin Talban Fika, Alhaji Baba Galadima a matsayin Bajangan Fika, Alhaji Ajiya Waziri a matsayin Iyan Fika da kuma Alhaji Muhammad Ciroma a matsayin Sarkin Noman Fika.

An yi wannan gagarumin biki ne a fadar Sarkin na Fika da ke ƙaramar Hukumar Potiskum a jihar Yobe ran asabar 12, ga watan Afrilun wannan shekara.

Jama’a sun yaba da zaƙulo waɗannan haziƙan mutane da suka yi fice wajen tallafawa jama’a da ciyar da ƙasa gaba.

Bikin naɗin sarautar ya ƙayatar inda makaɗa, mabusa da mahaya dawaki suka burge masu kallo.

Waɗanda aka naɗa sarautun sun yi mubayi’a ga Sarkin na Fika, kuma shugaban majalisar Sarakuna na jihar Yobe.

Sarakunan Bade, Tikau da Fune sun halarci bikin.

Bugu da ƙari, AM Muhammadu Dikko Umar ya yi jawabin godiya ga Sarki a madadin waɗanda aka naɗa wa sarautun, ya ce, “Ina jaddada mubayi’a da goyon baya ga Mai Martaba Sarki da majalisarsa don ƙara ciyar da masarauta da ƙasar Fika da Nijeriya bakiɗaya. Muna godiya da karrama mu da aka yi.”

Waɗanda aka naɗa sun hau dawaki daga Fada inda ‘yan uwa da abokan arziki suka yi musu marhabin.

Jama’a da yawa ne suka halarci bikin daga nan cikin gida har da ƙasashen waje.

By ukarofi