An kori malamar makaranta da ta yi ciki babu aure ba

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata makaranta mai zaman kanta ta kori wata malamar da ta yi ciki ba tare da aure ba.

Wani wanda ba a san sunansa ba ya ba da rahoton lamarin a dandalin microblogging a shafin Tiwita.

Wanda ba a bayyana sunan nasa ba ya ce makarantar ta yi ikirarin cewa za ta yi mummunar tasiri a kan ɗalibansu.

A cewar marubucin, malamar makarantar ta yi ciki kafin ta yi aure.

Yanzu haka dai makarantar ta kori malamar saboda fargabar halin da take ciki na iya shafar ɗalibai ta wata hanya.

An yi imanin cewa yin ciki ba tare da yin aure ba zai iya zama mummunan tasiri a kan ɗalibai mata na makarantar.

Rubutun ya ce; “Don Allah ko ya dace makarantar  ta kori malamar da ta yi ciki ba tare da aure ba don gudun yin illa ga ɗalibai mata? Ku bayyana ra’ayinku don Allah.”

Wannan ya haifar da ra’ayoyi daban-daban daga ‘yan Nijeriya da ke goyon bayan shawarar makarantar yayin da wasu ke ganin cewa ba lallai ne rayuwarta ta kasance ta shafi ɗalibai ba.

By ukarofi