Haɗaka: Wataƙila gwamnonin PDP na yi wa Tinubu aiki ne – Dele Momodu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi zargin cewa gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar da ke adawa da haɗakar jam’iyyun adawa wataƙila suna yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu aiki ne a ɓoye.

An rawaito cewa gwamnonin bayan ganawar da suka yi a birnin Ibadan a ranar Litinin da ta gabata sun yi watsi da yiwuwar haɗewa ko haɗaka da wata jam’iyyar siyasa gabanin zaɓen 2027.

Amma da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, Momodu ya ce babu ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun adawa da zai iya kada Tinubu a shi kaɗai a 2027.

Mawallafin Mujallar Oɓation ya shawarci ‘yan adawa da su haɗa kai su yi amfani da dabarun da APC ta yi amfani da su a shekarar 2015 wajen cin zaɓe.

“Shugabannin ‘yan adawa sun ƙuduri aniyar yin aiki tare a wannan karon, gaskiyar magana ita ce Atiku ba zai iya shi kaɗai ba, Peter Obi ma kuma shi kaɗai ba zai iya yi ba, kuma Rabi’u Kwankwanso ba zai iya shi kaɗai ba.

“Don haka, a zahiri, dole ne su lalubo hanyar da za su kada APC ta hanyar ƙoƙarin ganin an samu aƙalla gungun jam’iyyu uku.

“Idan gwamnoninmu suna cewa a’a, ba ma son shiga haɗa, to hakan yana nufin cewa a ɓoye ƙila suna yi wa shugaban ƙasa Tinubu aiki ne.

By ukarofi