Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A makon jiya ne Ministan Ilimi na Nijeriya, Mista Olatunji Alausa, ya yi kira da a tsawaita wa masu yi wa ƙasa hidima lokacinsu daga shekara ɗaya zuwa biyu.
Mista Alausa ya yi kiran ne a lokacin da Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa da NYSC ta wallafa a shafin sada zumunta na Facebook, ministan ya kuma yi kira da a faɗaɗa shirye-shiryen horar da sana’o’i da koyar da sana’o’i ga ‘yan NYSC.
“Ministan ya kuma bayar da shawarar tsawaita aikin hidimta wa ƙasa daga shekara ɗaya zuwa biyu, tare da faɗaɗa shirin horar da sana’o’i ga ‘yan NYSC,” inji sanarwar a wani ɓangare.
Ministan ya kuma bayar da shawarar tura ƙarin malaman da suka kammala karatu a makarantun karkara, yana mai cewa “hakan zai cike giɓin ma’aikata a makarantun.”
Ya yaba wa mahukuntan hukumar NYSC bisa himma da kuma na’urar tantance masu yi wa ƙasa hidima, da nufin daƙile badaƙalar satifiket da ta shafi wasu ɗaliban da suka kammala karatun digiri a ƙasashen waje a yammacin Afirka.
A halin da ake ciki dai, shawarar da ministan ya gabatar ta janyo cece-kuce daga ‘yan Nijeriya. Yayin da wasu suka nuna goyon bayansu ga ra’ayin, wasu kuma sun ce shawarar za ta nakasta matasa.
Yayin da ya ke zantawa da wakilin jaridar Blueprint, Farfesa a fannin ilimin zamantakewa, Yakubu Odekina, wanda yana cikin rukunin farko da aka tura a farkon shirin, ya ce yana goyon bayan shirin tsawaita hidimar.
Odekina ya ce, shirin NYSC gadon ƙasa ne kuma alama ce ta haɗin kan Nijeriya.
Ya ci gaba da cewa, ya kamata a kiyaye shirin na NYSC, tun da manufarsa ita ce inganta haɗin kan ƙasa a tsakanin ‘yan Nijeriya, waɗanda suke ciki.
“An kafa wannan shiri ne domin a cimma burin samar da haɗin kai a tsakanin ƙabilun Nijeriya, wanda hakan na aiki sosai.
“Ko kaɗan ba zan goyi bayan soke shi ba, domin baya ga haɗin kai, yana taimakawa matasa wajen ziyartar wasu sassan ƙasar nan.
“Yawanci, wasu daga cikin matasan ba za su sami damar yin balaguro zuwa wuraren ba, sai dai don shirin. Amma mafi muhimmanci, yana bawa matasa daga ko ina faɗin ƙasar damar yin hulɗa da wasu ƙabilu daban,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Maimakon a yi watsi da shirin, kamata ya yi gwamnati ta duba irin ƙalubalen da shirin ke fuskanta kamar rashin tsaro, haka kuma gwamnati za ta iya ƙoƙarin ganin ta sake fasalin tsarin domin ingantacciyar hanyar da za ta dace da kuma haɗa kai, za a iya mayar da shi cibiyar koyon sana’o’i ga matasa.
Haka zalika, wata kwararriya kan harkokin kasuwanci da ilimi, Dr. Dorothy Osamor, ta ce shirin ya zama abin koyi ga sauran ƙasashen Afirka.
Ta ce, “Abin ban sha’awa shi ne, a yayin da ministab ke bayar da shawarar a tsawaita wa’adin shekara ta hidima, wasu na kira da a soke shirin, suna ganin kamar ɓata lokaci ne, rashin tsaro ya ƙara dagula wannan kiran, ganin yadda wasu masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da ’yan NYSC a shekarar hidimarsu.
Sai dai wani masanin tattalin arziki, Uche Anyadike, ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi la’akari da tasirin tattalin arziki da zamantakewar wannan ƙudiri ga ƙasa da kuma matasan da suka kammala karatu.
Ya ce, biyan N77,000 ga masu yi wa ƙasa hidima daga Naira 33,000 a baya-bayan nan yana haifar da babbar illa ga tattalin arzikin ƙasa a kan tanadin kasafin kuɗin shirin. Ya ƙara da cewa, “gwamnatin tarayya na iya kashe kusan Naira biliyan 310 domin tara jama’a da alawus-alawus saboda ‘yan NYSC, nauyin kuɗi na iya yi wa gwamnatin tarayya yawa.”
Haka zalika, wani mai sharhi kan al’umma, Dokta Olu Ibidapo, ya ce ba ya goyon bayan tsawaitawa ko kuma a bar shirin kamar yadda yake, amma ya yi kira da a sake fasalin tsarin.
