An fitar da takardar bayani a wajen babban taron yanar gizo na duniya na shekara ta 2022

Daga CMG HAUSA

Da maraicen yau Laraba 9 ga wata ne, a wajen taron ƙolin Wuzhen na babban taron yanar gizo na duniya na shekara ta 2022, cibiyar nazarin kafar yanar gizo ta intanet ta ƙasar Sin, ta fitar da takardar bayani kan rahoto game da ci gaban yanar gizo ta ƙasar Sin na shekara ta 2022, da rahoto game da ci gaban yanar gizo ta duniya na shekara ta 2022.

Tun daga shekara ta 2017, an fitar da irin wannan takardar bayani zuwa ga duk faɗin duniya a cikin jerin shekaru shida, matakin da ya kasance wani muhimmin ɓangare na babban taron yanar gizo na duniya.

Takadar bayanin, wani muhimmin sakamakon nazari ne da aka yi, wadda cibiyar nazarin kafar yanar gizo ta intanet ta ƙasar Sin, da sauran wasu cibiyoyin ƙwararrun nazarin ɓangaren yanar gizo na gida da na waje suka tsara cikin haɗin-gwiwa, inda aka nuna sabon ci gaba, da sabbin nasarorin da aka samu a ɓangaren bunƙasa harkokin yanar gizo ta intanet.

Mai fassara: Murtala Zhang