Dabara ta rage ga mai shiga rijiya

Daga IBRAHIM YAYA

Yanzu haka ana gudanar da taron ƙasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MƊD ko COP27 a taƙaice, a wurin shakatawa na Sham El-Sheikh dake ƙasar Masar, inda shugabannin ƙasashen duniya za su tattauna kan matsalolin dake hana ruwa gudu game da magance matsalar sauyin yanayi dake ci gaba da addabar sassan duniya ta fannoni daban-daban.

Galibin shugabannin ƙasashen da suka gabatar da jawabai a taron na wannan karo, sun ƙara yin kira ne ga ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, da su ɗauki matakai na zahiri maimakon maganar fatar baki da suka saba yi a duk lokacin da aka kira irin wannan taro ko wani dandali mai kama da wannan, domin shawo kan illolin da sauyin yanayin ke haifarwa, kamar zafi da fari da ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa dake tafe da mamakon ruwan sama da makamantansu.

Haka kuma sun yi kashedin cewa, lokaci fa yana ƙurewa, kuma duk wani jan kafa kan wannan batu, babu abin zai haifar illa haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Yanzu haka ana kiyasin cewa, mutane miliyan 700, za su rasa muhallansu a nahiyar Afirka, sakamakon rashin ruwan sha nan da shekarar 2030.
Shi ma babban sakataren MƊD Antonio Gutteres, ya shaidawa taron cewa, duniya ta doshi hanyar shiga bala’u na sauyin yanayi, wanda kusan kowa yana ganinsu a sassan duniya, kamar irin matsalolin da aka ambata a sama na ambaliyar ruwa da matsanancin fari da sauransu.

Wani rahoto da hukumar kula da makamashi ta MƊD ya nuna cewa, a shekaru 8 dake tafe, ana iya cewa, duniya ta kama hanyar fuskantar zafi mafi tsanani a tarihi. Shin ina muka dosa?

Hukumomin MƊD gami da ƙungiyoyi masu zaman kansu ma, sun yi kashedin cewa, an samu ƙaruwar matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a cikin shirye-shiryen kula da abinci mai gina jiki a fadin yankin ƙahon Afirka, wannan ma wata alama ce ta matsalar sauyin yanayi, haka kuma mutane da dama sun rasa abubuwansu na rayuwa, da hanyoyin da za su iya magance wannan bala’i, sannan kuma sun dogara baki ɗaya kan taimako don biyan bukatunsu na yau da kullum, matakin da zai iya ƙalubalantar farfaɗowar fari.

Yanzu dai dabara ta rage ga mai shiga rijiya.

Ko dai duniya ta mayar da hankali wajen ɗaukar managartan matakan magance wannan matsala ko kuma duniya ta ci gaba da shiga hali na garari sakamakon matsalar sauyin yanayi.