Yau ake zaɓen ƙananan hukumomi a Neja

Daga WAKILINMU

Yau Gwamnatin Jihar Neja take gudanar da zaben Kananan Hukumomi a faɗin jihar.

Tuni Gwamnan jihar, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ayyana ranar a matsayin ranar hutu don bai wa jama’a damar fita zuwa wajen zaɓe.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar da ta fito ta bakin Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane.

Sakataren ya ce yayin zaben, kasuwanni da ma’aikatu za su kasance a rufe, sannan za a hana zirga-zirgar ababen hawa amma ban da masu ayyuka na musamman.

A cewar Matane, “Gwamnati na kira ga ‘yan jihar da kowa ya fita ya sauke nauyin da ya rataya a kansa a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamban 2022.

“Wannan lokaci ne da za mu fita mu zabi wakilai da shugabannin da za su jagorance mu a matakin Kananan Hukumomi.”

Sanarwar ta ce, Gwamna Sani Bello ya umarci daukacin hukumomin tsaron jihar da su tabbatar ba a samu wani akasi a yayin zaben ba.