Tun bayan ɗarewa kan kujerar shugabancin ƙasa da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ‘yan Nijeriya ke ta annushuwa da farin cikin Nijeriya ta yi sabon angon da zai ceto ta daga durƙushewa, amma sai a ka ga saɓanin haka. Abinda ya jefa ‘yan ƙasa cikin taraddadi da halin-ni-‘ya-su, ya kuma saka ‘yan ƙasa tagumi da zullumin abinda ka je, ya zo. Da dama wasu suna ganin lokacin da zasu samu sauƙi ya zo, wasu kuma suna shakkar hakan. Domin wasu kan ce, “BA A SAN MA CI TUWO BA, SAI MIYA TA ƘARE”.
Shugaba Buhari ya raba muqamai masu yawa a yankin Arewa, kuma duk ya raba su ne ga ‘yan Arewa domin su wakilci al’ummarsu domin ganin an gudu tare, an tsira tare. Tunda dai shi ma ɗan Arewa ne ba bare ba.
To amma abin tambayar a nan shi ne, shin wakilan yankin Arewa sun yi aikinsu yadda ya dace su yi shi ga al’ummar Arewar don a ciyar da ƙasar gaba, ko kuma dai sun yi shakulatin vangaro ne don a fake da guzuma a harbi karsana? Shin matsalar taɓarɓarewar Arewa daga shugaban ƙasa ne ko kuwa daga wakilan Arewa ne? wannan ita ce tambayar farko da ya kamata mu yi.
Kama daga Gwamnoni da Ministoci da sauran muƙamai kala-kala da ‘yan Arewa suka samu, wanda kowa ya ga irin tarin muƙamai da yankin Arewa ta ci gajiyarsu a shekaru huɗun baya na mulkin Buhari, da kuma shekaru huɗun ƙarshe da muke ciki a yanzu.
To don haka, matsalolin da suke faruwa a yankin Arewa daga ina matsalar take? Kuɗin da Gwamnati ke kasaftawa a shekara-shekara, da tarin makaman yaƙi da ake sayowa, da ƙarin ma’aikata da ɗaukar sabbin jami’an tsaro, amma me ya sa yankin Arewa ya samu tangarɗa?
Idan muka ture duk wata adawa, muka tsaya muka kalli komai a tsanake, to tabbas al’amarin tafiyar da shugabancin ƙasarmu Nijeriya akwai Lauje cikin naɗi, akwai bara-gurbin abubuwan da suke wakana da aka yi wa talakawa lulluɓin biri (wai kura da fatar akuya).
Ga duk wanda yake bibiyar halin da ƙasarmu Nijeriya ke ciki a wannan mulkin na Muhammadu Buhari, yana ganin irin tarin maqudan kuɗaɗen da Gwamnati ke tarawa, domin ga misali nan a kasafin kuɗi da ake gabatarwa ga majalisar ƙasa.
Kuɗi ne waɗanda tunda aka gina Nijeriya babu wata Gwamnatin Soja ko ta farar hula da ta tava gabatarwa ga majalisar ƙasa. Amma hakan bai hana ‘yan Nijeriya shiga cikin taskun rayuwa da halin qa-ƙa-ni-ka-yi ba, hakan bai hana talakawa da dama rataye kansu ba, hakan bai kawo dakatuwar karɓar cin hanci da rashawa ba.
A shekarun baya, Nijeriya ba ta da yawan matatun man fetur da za su haƙo mai, amma kuma ‘yan ƙasa basa shan wahala a kansa. Hakazalika, babu manya-manyan gidajen wutar lantarki, amma wutar ta wadaci ko’ina.
Babu yawan asibitoci da makarantu, amma talakawa suna amfana daga asibitin Gwamnati, yara za su je makaranta suyi karatu duk da babu wadatattun Malamai. Babu yawan jami’an tsaro amma tsaro ya inganta, babu yawan kasuwanni amma kasuwanci yana da albarka, babu yawan motocin sufuri da titina amma ‘yan ƙasa basa shan wahalar yin fatauci da tafiye-tafiye don gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
Yanzu da Nijeriya take cikin jerin ƙasashen da suka haɓaka wajen yawan tattalin arzikin ƙasa da yawan al’umma, amma kuma kullum talakawa faɗi suke yi “Gara jiya da yau”, shin me ya sa haka?
Darajar kuɗin ƙasarmu ya mutu, kasuwanci ya lalace, ilimi ya taɓarɓace, babu tsaro, babu wadatacciyar wutar lantarki, babu tsaftataccen ruwan sha, babu wadataccen magani a asibitocin ƙasarmu, shin me ya kawo haka? bayan kuma an samu wayewa, da tarin dukiyar da za mu iya ciyar da ƙasarmu har da sauran wasu ƙasashen.
Sai dai kuma hakan bai hana ‘yan ƙasa cin guba suna mutuwa ba, wasu su rataye kansu, wasu su yi sata a kashe su, wasu su ɗauki makami su tare hanya, su yi qwace har da kisa, wasu su haura gidaje, wasu su fasa bankuna da shagunan kasuwanni su yi sata. Idan akwai cigaba a ƙasa, to me zai sa ɗan ƙasa ya je ya yi wannan?.
Don haka, idan har waɗannan matsalolin suna fitowa ne daga shugaban ƙasa, to menene amfanin waɗanda suke taimaka masa wajen gudanar da mulkin? Domin kuwa masu azancin magana suna cewa; “Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka”. Tabbas kuma wannan magana haka take, idan Ɓera da sata, to Daddawa ma da wari. Shi ya sa aka ce, “Ba a mugun Sarki, sai dai mugun bafade.
Idan har Gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaza wajen kyautata rayuwar ‘yan qasa, to mu sani cewa lallai ba shi kaɗai ya gaza ba, kuma waɗanda suka fi gazawa su ne wakilan al’umma. Su ne manya-manyan maciya amanar ƙasa da ‘yan ƙasa.
Sai dai kuskuren farko da za a iya danganata shugaban ƙasa da shi, ba wuce rashin tsayawa ya tantance su waye ya kamata su taimaka masa wajen ganin an saita ƙasar nan ta hau kan gwadabe na haƙiƙa ba. Ba za a ce shugaba Buhari bai yi wani abu ba, amma dai tabbas wakilan jama’a sun ci amanar talakawa.
Kuma wannan ta faru ne sakamakon rashin tabbatar da doka da oda, duk abinda mutum yayi na sata da almundahana a yayin da yake kan kujerar mulki, to babu mai bincikensa.
Idan kuwa har kaga an bincike shi, to kawai ɗan wata jam’iyya ne daban ba wadda take mulki ba. Kamar dai yadda a wannan gwamnatin muka sha gani sau da dama. Har ta kai ta kawo mataimakin shugaban ƙasa yana ikirarin babu masu faɗa wa gwamnatinsu gaskiya.
Saboda haka kenan ita kanta Gwamnatin ta san bata kan dai-dai, tunda ga shi har ana neman waɗanda za su faɗa mata gaskiya. Shari’a bata aiki sai a kan talakawa, jami’an tsaro ba sa tursasa kowa sai talaka. Kana so, ba ka so, haka za a ɗauko wani a ɗora shi a kan mulki sai dai idan mutuwa za ka yi ka mutu.
A Arewa ne aka ƙirƙiri Boko Haram, an kashe rayuka, an ɓarnatar da dukiyar al’umma ba kaɗan ba, amma tamkar wasan kwaikwayo. Wata ƙabila ta ɗauki makami tana satar mutane ana neman kuɗin fansa, shi ma al’amarin ya zamo tamkar wasan kwaikwayo a cikin majigi.
Yara da yawa ba sa zuwa makaranta a yankin Arewa, mata da yawa sun zamo Zawarawa a sanadin kashe mazajensu, mafi yawa daga cikinsu, rayuwa ta yi matuƙar tsadar da hakan yake haifar da ciwon zuciya da kwana da yunwa.
Don haka, dole a cikin biyu a samu ɗaya, ko dai Shugaba Buhari ya yi duk abin da ya dace, amma abokan aikinsa ne suke masa zagon ƙasa, yana tufka suna warwara, ko kuma bai yi abinda ya dace ba su ma suka bi yarima suke shan kiɗa. Amma ba zai yiwu a ce duka an taru an zamo ɗaya ba, dole akwai babba ko a gidan Giya, wanda idan ya tsawatar a kan abinda ake yi na ba dai-dai ba, ake dakatawa.
To mu dai ba mu san halin da zamu tsinci kanmu a nan gaba ba a yankinmu na Arewa, babu wani ɗan Arewa dake yin bacci cikin salama da kyakkyawan yaƙinin babu abinda zai same shi. Hakazalika, babu wani ɗan Arewa da yake yin balaguro da tabbacin zai dawo ga iyalansa lafiya.
Shin zai yiwu a ce talakawa su za su kare kansu daga dukkan wani ɗan ta’adda mai riƙe da makami? Ko kuwa dai Gwamnati ce tare da muqarrabanta za su yi duk mai yiwuwa don ganin sun kare al’umma ta yadda za su yi rayuwa cikin aminci.
Tilas ne mu yi kukan rashin adalci a cikin mulkin da al’umma suke kasa cin abinci sau uku a kullum don su rayu, a yayin da kake yin fafutukar hakan, to za ka iya zama babu kai a doron ƙasa. Domin duk wani abu da a da ka fi ƙarfinsa, to yanzu shi ne ya fi ƙarfinka sai ɗai-ɗai.
Talauci da fatara gami da ƙuncin rayuwar dake koara ta’azzara ta jefa talakawa cikin mawuyacin halin da za a ɗauki shekaru da dama kafin talaka ya dawo hayyacinsa (musamman a yankin Arewacin Nijeriya).
Da wannan nake cewa, ƙalubalenku masu mulki.
Nafiu Salisu
Marubuci/Manazarci. Adireshin Imel:
[email protected]
[email protected]
08038981211
