Daga BELLO MUHAMMAD SHARAƊA
A shekara bakwai da watanni na mulkin Najeriya a karkashin tutar jam’iyyar APC:
- Ba su gyara wutar lantarki ba.
- Ba su gyara tsaron Rai ba.
- Ba su gyara tsaron dukiyar jama’a ba.
- Ba su gyara harkar lafiya da ilimi ba.
- Ba su gyara musibar rashawa ba.
6.Ba su gyara tsadar abinci da kayan noma ba. - Ba su gyara hauhawar farashin kayan masarufi ba.
- Ba su gyara darajar Naira da tashin Dala ba.
- Ba su gyara hanyoyin sufurin sama da qasa da ruwa ba.
- Ba su gyara aikin gwamnati ba a kowanne mataki
- Sun yi alƙawurra ba su cika ba. An ba su amana sun ci. A duk zancen da za su yi sai sun yi ƙarya.
- A jihohin Arewa da kudu, guda 36 har da Abuja
37, an zavi APC a jiha 26 a shekarar 2015. A yanzu akwai gwamnonin APC a jiha 24, amma babu jihar da ba a kuka da mulkin APC. - Babu jihar da APC bata dagula lissafin jama’a ba.
- Babu jihar da mutanen jihar ba su yi Allah wadarai da gwamnatin APC ba.
A zaɓen shekarar 2023 APC sai an bata wuta! Idan ta gama shan wuta, sai kore ta daga kan mulki.
Bello Muhammad Sharaɗa, masani ne kuma mai sharhi a kan al’amurran siyasa. Ya rubuto daga jihar Kano.