Samar da ƙwararrun ma’aikata da kayan aiki ne sirrin nasarar kowacce makaranta – Dakta Sulaiman

Daga BABANGIDA S.GORA a Kano

Kwalejin koyon aikin jinya ta Emirates dake jihar Kano, Kwalejin ce wacce aka kafa kwanan nan don Bunƙasar harkokin ilimi a Arewacin Nijeriya, sannan wannan makaranta ta yi suna a cikin jihar Kano da ma maƙwabtan jihohi. Dakta Shu’aibu Sulaiman shi ne Daraktan makarantar Emirates. A hirar da da wakilin Blueprint Manhaja, Babangida S. Gora, ya feɗe mana biri har wutsiya game da yadda aka samar da ita, da kuma yadda al’amuran suke tafiya a game da ita. Sai a biyo mu don jin cikakken bayani.

BLUEPRINT MANHAJA: Ka fara gabatar mana da kanka.

DAKTA SHU’AIBU SULAIMAN:  Sunana Shu’aibu Sulaiman, kuma Shugaban kwalejin koyon aikin lafiya, watau Emirate Collage of Health Science and Technology dake nan Tudun Yola, Jihar Kano.

Mene ne dalilin kafa wannan makaranta?

To, Alhamdulillah, kullum idan aka yi min tambaya irin wannan, tana yi min daɗi. Kwalejin Emirate dai ashekarar 2013-2014 aka fara tunanin kafa ta.  Wannan kuma ya samu bayan wani ɗan bincike da muka kafa kwamitin mutane bakwai da samun matsaya na ko a gina makaranta ta Sakandire amma wadda za ta amsa sunanta a ƙasa, ko Kuma a gina makaranta ta kimiya da fasaha watau ‘Polytechnic’, ko Kuma kwalejin Lafiya irin wannan. To komai za ka yi idan ka yi amfani da ilimi da masu ilimi cikin harkokinka, daga ƙarshe kusan a kwashanniya da muka raba kashi 81% da ɗigwani da aka samu na ra’ayoyi ya karkata ga gina kwalejin Lafiya a wannan yanki ya fi dacewa da ita.

Saboda muna da ƙarancin ma’aikatan lafiya a yankunanmu da Kano, wanda nan take muka tura wa waɗanda suka buƙaci za su yi. Kuma cikin ikon Allah, yau gashi muna tafiyar da ita, kuma su waɗanda suka buƙaci za su yi wannan makaranta kasancewar sun yi zaman aiki a kudanci ƙasar nan sun ga jihar da ba ta kai Kano ba ma, kama daga jami’a da kwaleji irin wannan sai kasamu sama da 20 a jiha ɗaya. Don haka, suka ga ya kamata tunda sun samu dama su ma su bada tasu gudunmuwar a yankinsu.

A Jihar Kano ne kawai kuke da wannan makarantar ko akwai ta a wasu johohin ƙasar nan?

To, muna da ƙudurin faɗaɗa wannan makaranta zuwa wasu jihohin saboda irin kiraye-kiraye da jama’a ke ta yi mana. Musamman zan yi amfani da wannan dama na miƙa saƙon godiyarmu ga mai girma gwamnan jihar Sokoto, Dakta Aminu Waziri Tambuwal, don da ya kawo mana ziyara wannan makaranta, ya ga irin kayan aiki da muke da su a ƙasa, ya yaba. Ya ce mu je Sokoto mu gina reshen Emirate Collage a jiharsa, wanda ya ba mu fili kyauta, da yanzu haka shirye-shirye yayi nisa.

Sannan kuma kafin mu kammala ginin makarantar Emirate a Sokoto, Tambuwal ya kawo ɗaliban sokoto da yanzu haka suna nan kwalejin Emirate ta Kano suna karatu mutum 60. Wasu da karanta digiri, wasu Kuma difiloma. Don muna da vangarori guda biyu. Haka kuma Jihar Jigawa ma yanzu haka muna shirin gina College of Nursing da zamu buɗe a Jigawa insha Allahu.

Cikin bayanin da ka yi cewa, makarantar na da sassa biyu. Ko za ka yi mana ƙarin haske a kan hakan?

Alhamdullahi, ka san tsarin makarantu daban-daban ne. Na farko tsarin jami’a, na biyu akwai tsarin Polytechnic, sai tsarin Kwaleji. To mu nan tsarin Kwaleji ne amma tun daga farko muka yi tsarin jami’a ne.

Don haka, kayan aikinmu na jami’a ne, don muna da buƙatar yin digirin ne. Bayan mun yi  shekaru biyar da fara difiloma, muna ganin idan yaranmu sun gama, to ta yaya za su samu waɗanda suke buƙatar cigaba zuwa digiri a nan BUK har UDUs Sokoto mun bibiye su mun nema masu gurbin karatu sun cigaba.

A yanzu haka, sashen haɗa magunguna na BUK muna da ɗalibai da sun samu gurbi a nan. Da muka ga haka, muka yi tunanin yadda za mu sama wa ɗalibanmu sauƙi wanda suke buƙatar cigaba da digiri, sai muka sa binciken Jami’ar da za mu haɗa gwuiwa da su.

Muna cikin binciken ne, har Allah ya kai mu Jami’ar jihar Kwara, inda muka rubuta musu takarda suka ce to, za su turo wakilansu, don su zo duba makarantarmu, su ga idan mun cancanta da za su iya haɗa gwuiwa da mu. Nan suka turo wakilansu suka zo inda muke, muka yi kwana biyu da su.

Bayan sun gama duba dukkan abinda ya kamata, suka koma. Bayan wasu kwanaki, muka samu takarda cewa, sun amince da haɗakarmu, suka sama mana rana daga nan Kano, mu ma muka kama hanya kusan mu huɗu ko uku muka isa Kwara. Cikin ikon Allah bayan mun gama ganawa da su, muka sa hannu tare da ƙulla alaƙa da cewa, za mu rinƙa gudanar da karatun digiri ta ƙarƙashin Jami’arsu na darussa guda huɗu, kafin alaƙar ta cigaba, sai an samu yarjewar Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).

Babu ɓata lokaci muka rubuta takarda zuwa NUC domin zuwa a duba idan mun cancanta a sahale mana, idan kuma, inda muke da gyara kuma, a ce mu gyara. Idan ma bamu cancanta ba, a ce mu bari, sai mun shirya. to cikin hukuncin Allah dai, mun samu amincewarsu bayan sun zo. Su ma sun duba duk abinda suke buƙata, bayan ta turo farfesoshi guda uku, su ma suka rubuta wa JAMB da NYSC suna sane da yarjewa tsakin Jami’ar Kwara da Emirate Collage Kano wajen haɗakar gudanarwa ta karatu.

Waɗanne ƙalubale Emirates ta fuskanta yayin buɗe ta?

Wallahi Gaskiya ne! Akwai ƙalubale ba kaɗan ba, kuluma ba ƙanana ba. Ko mu a wannan makaranta a shekara ɗaya zuwa ta biyu ta farkon buɗe ta, an kusa rufe wannan makaranta, don ƙalubalen.

Wasu ana iya tsammaninsu, wasu kuma suna zuwa bagatatan. Amma da taimakon Allah da shawarwarin mutane, aka ce a duba niyyar da aka yi tun farko. Don haka za a yi, ba don wani abu daban ba. Kuma akwai buƙatu da yawa da suke buƙatar kayan aiki kusan za mu iya cewa kuɗi, da mu kanmu ƙalubalen su kansu ɗaliban ne.

Domin kuwa ko da yaushe abinda suke kallo shi ne, ai makarantar ta kuɗi ce. Ma’ana, kuxi suke biya, babu wanda ya isa ya hana su yin abinda suke son yi. Don haka, akwai ƙalubalen da da yawa babu lokacin da za mu bayyana su. haka kuma, ba mu amince malami ya ci zarafin ɗalibi ba, shi ma ɗalibi ba zai ci mutuncin ma’aikatanmu ba, ko da mai shara ne. Kuma mu a nan ba karatu kaɗai muke badawa ba, akwai tarbiyya da sauran abinda ya kamata ya taimaka masu har tsawon rayuwarsu.

Mun fuskanci abubuwa da dama wanda da yawa lokacin da muka fara wasu na ce wa ɗalibanmu, idan kun je kun yi karatun nan da takardaku da ta tsire duk ɗaya ne, ba ta da wani amfani. Amma a haka muka yi ta yi wa jama’a bayani da ƙarin hasken da zai taimaka mana, har al’umma suka fahimci yadda muke, da abinda muke so.

Wanne irin kira za ka yi wa sauran masu kwalejin irin naku wajen tsaftace ayyukansu?

Maganar karatun lafiya abu guda biyu ne. Na ɗaya shi ne, dole ka samar masa da ƙwararrun malamai,  kuma dole ka samar da kayan aiki. Mu kuma alhamdullahi a nan zan so na qara godiya ga gwamnati jihar kano ƙarƙashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, bisa irin ƙoƙarinsu wajen magance matsalolin rashin samun sahihanci ilimi a jihar.

Yanzu maganar da muke da kai, gwamnati jihar ta samar da wani kwamitin da zai duba cancantar jami’o’i da kwaleji masu zaman kansu don tabbatar da cewa, ko sun cancanta, ko kuwa ba su dace ba, wanda ni kaina ina cikin wannan kwamitin. Daga ƙarshe da muka yi aik,  muka miƙa aka duba, sai da gwamnati ta rufe makarantu guda kusan 20 da wani abu.

Don haka, gwamnatin jihar ta yi ƙoƙari, sannan mun bada shawarwari kan duk wanda zai gina makaranta ga irin ƙa’idojin da ya kamata a gindaya masa, kafin ma masu ruwa da tsaki kan abun abin shigo ciki.

Kuma mu ma da ake ganin muna cika sharuɗɗan da ake so, ya kamata a rinƙa bibiyar mu da ganin yadda muke, ba wai a ƙyale mu ba a sa mana lokaci. Bayan don tabbatar da aikinmu yana tafiya dai-dai. A nan, ina ba sauran ‘yanuwana masu tafiyar da irin wannan makarantu da su yi abinda ya kamata don samar da kyakkyawan ƙarshe.

Dakta, ko akwai wani abu da za ka qara wa jama’a masaniya a kansa?

Na farko zan yi wa Allah godiya bisa nasarar duk abinda muka ƙudurta kan kafa wannan makaranta ɗaya bayan ɗaya, muna samun nasararsu. Sai kuma abin farin cikina a nan shi ne, yadda aƙalla mutane 80 wanda suke cin abinci a wannan makaranta daga ƙananun ma’aikata zuwa manya kuma cikinsu kowanne yana da iyali da suke cin abinci a ƙasansa. Idan ka tara mutum na kenan.

Ko nan bakin get ka duba, mutum nawa ke cin abinci ta hanyar Hotokwafe, da sauran abubuwan da ake sayarwa. Ka ga ko nan an ɗauke ma mutane rashin aikin yi. Kuma abin alfahari shi ne yadda bana da gwamnati jihar Kano ta ɗauki ma’aikatan lafiya kusan asibiti ɗaiɗaiku ne babu ɗaliban Emirate a cikinsu. Ka ga wannan nasara ce babba, sannan ko da yaushe sai kana neman shawarwari daga jama’a, haka kuma ƙofarmu a buɗe take ga duk wanda ya ga muna da gyara ga lambar wayar a ko’ina ya kira mu don yi mana gyara.

Kuma muna maraba da su, kuma za mu yi godiya ta musamman ga iyayen yaran da suke kawo mana ya’yansu a matsayin amana. Kuma Insha’Allah, za mu cigaba da bakin ƙoƙarinmu wajen samar da ingantaccen ilimi da zai taimaka ƙasarmu da al’ummarmu.

To, mun gode.

Mu ma mun gode.