Bai dace a ce marubuci na da keɓantaccen salo da aka san shi da shi ba – Hadiza Auta

“Rubutun barkwanci yana sa nishaɗi a zuciyar mai karatu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A jerin hirarrakin da muke kawo muku da wasu fitattun marubuta da suka yi fice a wasu ɓangarori na rubutun adabi, har kuma aka san su kan wani salo na musamman da ke jan hankalin masu karatu ga rubuce rubucen su, yau shafin Adabi ya zaƙulo muku wata marubuciya ne da masu karatu da abokan rubutun ta suka karyawa kallabi, saboda ƙoƙarin ta wajen nishaɗantar da masu karatu, da salon ta na rubutun barkwanci. Marubuciya Hadiza D. Auta daga Jihar Zamfara ta shahara wajen rubutun labaran ban dariya da rikita rikitar zaman aure da makirce makircen zaman iyali. A tsukin shekaru uku da ta yi da kasancewar ta a cikin duniyar marubuta, Hadiza Auta ta rubuta littattafai da gajerun labarai fiye da ashirin. A ganawarta da wakilin Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana masa babban burin da ta ke son ganin ta cimma, a wannan harka ta rubutun adabi. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?

HADIZA: Cikakken sunana dai Hadiza Ibrahim D. Auta, shi ne kuma sunan da aka fi sani na da shi. Ni marubuciya ce daga Jihar Sakkwato, amma asalin tushena shi ne Jihar Zamfara, daga qaramar Hukumar Qauran Namoda. Sannan kuma ni ýar kasuwa ce, Ina kuma sana’ar ɗinki.

Ko za ki ba mu tarihin rayuwarki a taƙaice?

Kamar yadda na ce ni asalina ýar Jihar Zamfara ce, amma rayuwata ta fi ƙarfi a Jihar Sakkwato. A Sakkwato aka haife ni, kuma a can na tashi. Sai daga baya ne na koma asalin Jihata ta Zamfara. A nan ne na ci gaba gaba da karatuna tun daga matakin farko har zuwa Diploma. Ni matar aure ce, kuma uwa, Ina da yara huɗu.

Gaya mana yadda ki ka fara rubutu da abin da ke baki sha’awa a harkar rubutun adabi?

Na fara rubutu a yanar gizo a shekarar 2019 ta sanadin yawan karance-karancen da nake yi, tun Ina yin karatun littattafan takarda har na dawo karanta na yanar gizo. Kasancewar daman can Ina tava ‘yan rubuce-rubucena tun Ina ƙaramar sakandare. Idan ban manta ba na rubuta littattafai sama da huɗu, daga cikinsu na so buga wani Allah bai nufa ba. Dalilin hakan lokacin da na zo yanar gizo na ga irin faxi-tashin da marubutan lokacin suke yi. Sai abin ya ɗarsa min sha’awar na dawo da rubutuna ta hanyar yanar gizo.

Akwai wata marubuciya mai suna Khadija Usman marubuciyar littafin ‘Tamaigari’. Ba na mantawa muna hirar littafinta nake sanar da ita ni ma Ina rubutu. Ita ce mace ta farko da ta fara ba ni ƙarfin gwiwa a kan na ci gaba da rubutuna. Amma a take na nuna mata ba zan iya ba saboda ban da masaniyar komai dangane da rubutun yanar gizo. Bayan ɗan lokaci sai kuma na ji sha’awar rubutun ya kama ni. Na zauna na yi guntun fejin rubutu na saka wa labarin suna ”Tartsatsi”.

Wanene ya fara koya miki yadda za ki fara hawa matakin farko na zamewarki marubuciya, wanda ba za ki mantawa da shi ko ita ba?

A lokacin da na yi rubutun na tura wa wasu aminaina, suka yi ta murna suna faɗin labari ya yi daxi a ƙaro wani. Daga nan na tura wa ƙanwata Billy S. Fari na ce ta duba mini da gaske wai ya yi kuwa, don a lokacin ita ma marubuciya ce tana rubutun. Cike da ƙarfafa gwiwa ta sanar da ni ya yi har ma ta nuna mini wasu abubuwan da ya dace mai rubutu ya sani kafin komai. Na yi murna sosai na je na ƙara yin wani sabon feji na turo mata. Sosai ta yi mamakin yadda na fito da duk abin da ta koya mini raɗau babu buƙatar wata bita. Daga haka na ci gaba da rubuta littafin tana ƙara ɗora ni a kan hanya, musamman Hausar Baka da nake amfani da ita a rubutuna, tun da ta sanar da ni ba a buqatar Hausar mutum na kiyaye, na dawo yin wadda nake ganin kamar ita ce daidaitacciyar Hausa ta rubutu.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa, bamu sunayen su da ɗan bayani a kan wasun su?

Na rubuta cikakkun littattafai goma sha uku. Sai gajerun labarai sama da goma sha. Daga cikin su akwai ‘Tartsatsi’, ‘Ruwa Da Ƙanƙara’, ‘Bakan Gizo’, ‘Baƙon Yanayi’,’Dije Ƙarangiya’, ‘Gidan Aure’, ‘Jiki Da Jini’, ‘Shagalalliya’, ‘Dace Da Juna’, ‘Musayar Zuciya’, ‘Amfanin Fitila, ‘Zubar Hawayena’, sai ‘Makarantar So’.

‘Baƙon Yanayi’, labari ne a kan wasu ‘yan biyu masu kama da juna sak-da-sak wato Munara da Munawwara. Sai dai kuma masu savanin ra’ayi da savanin fahimta, hakan ya janyo rashin jituwa a tsakaninsu, kasantuwar ɗaya tsagera ce ɗaya kuma mai sanyin hali. Dalilin mugun halin Munara ta yi sake Munawwara ta ƙwace zuciyar saurayin da take haukar so da kyawawan halayenta nagartattu. Saboda basajar da ya yi ya zo musu a ƙasƙantaccen mutum wulaƙantacce kuma abin ƙyama.

A tashi ɗaya Munara ta kwaɗa masa mari tun a ranar farko da ya kawo mata ziyara gidansu, bayan cin fuska da cin zarafin da ya sha a hannunta ba tare da ta san shi ne ba. Munawwara kuma ta karɓe sa hannu bibbiyu cike da tausayawa, saboda rauninta da zuciyar tausayi da Allah ya azurta ta da samu. Ita ma sai da ya yi mata nata gwajin ya turo abokinsa wurinta a cikin rigar arziƙi kuma hamshaƙin mai kuɗi.

Amma duk da hakan sai da ta tsallake rijiya da baya ta canye jarabawarsa ba tare da ta sani ba. An yi ruguntsumi da gwarama iri-iri a cikin littafin musamman a lokacin da liƙin ya buɗe gaskiya ta bayyana, har ya fito musu da kyakkyawar sifarsa ta asali, da kuma yadda yake a ɓangaren matakin Naira da tushensa na arziƙi.

Munara ta haukace sosai a kansu duka ta ko’ina kai musu sara take yi suna kaucewa, sai dai kasantuwar kamar da take yi da Munawwara ta shige rigar kamanceceniya ta yi ta yaƙar aurensu ta ƙarƙashin ƙasa har ta yi nasarar raba musu aure.

‘Ruwa Da Ƙanƙara’ kuwa littafin ne da ya ƙumshi rashin halaccin maza idan suka yi sabon aure, musamman ga matayen da ba su tava haihuwa ba, waɗanda idan suka samu haihuwar da amaryarsu su juya wa uwargida baya, kuma su manta ce wa Allah ne ke ba da haihuwa ba qarfi ba.

Wannan duhun baƙin cikin shi ya assasa tushen labarin Uwargida ta sace jaririyar da aka haifa ta jefar daji tun tana cikin tsumman goyonta. Ta yi rayuwa a hagunce duk da uban riƙon da ta samu managarci ne. Kafin daga baya bayyanar iyayenta ya wankar da ƙuncin rayuwar da ta fuskanta a baya.

Shi kuwa ‘Zubar Hawaye’ labari ne da ke nuna tsantsar butulci ga rayuwar wanda aka yi wa halacci. Bayan son zuciya da ya janyo silar ruguje rayuwar ahalin ya tarwatsa farin cikin masu gidan da mazauna gidan gaba ɗaya. Ta sanadin hakan ya yi tsanin kashe matar gidan, aka yi garkuwa da ‘yar gidan har ya yi mata fyaɗe ta haife masa ‘yar da ƙyar, saboda zawarcin neman rayuwarta da ya sha yi, amma Allah bai sa ya yi nasara ba, bayan gudun famfalaqin da ta sha a rayuwa da firgici a kan duk wanda ya rave ta sai rayuwarsa ta shiga garari.

Bayan hakan ya haukatar da mahaifinta ya auri ƙanwarta. Saboda sanadinta ne ya nemi halaka kowa domin ya same ta. Sai ga shi daga baya duniya ta yi masa juyin waina ya dawo abin tausayi abin ƙyama kafin hukuncin kisa ya tabbata kansa.

Wanne littafin ne silar samun ɗaukakar da ya sa aka fara sanin ki, kuma mai ya bambanta shi da sauran labaran da ki ke rubutawa?

‘Dije Ƙarangiya’ shi ne littafin da ya fito da ni kowa ya san da wanzuwar sunana a cikin marubuta da masu karatu dukka. Bambancinsa da sauran littattafaina shi ne barkwanci, domin a dukka labaraina Ina taɓo wasu manyan jigon da ke addabar mutane a wannan lokacin da muke ciki na yi rubutu mai kama da wa’azantarwa.

Saɓanin littafin da salonsa ya zo da nishaɗi har ma da guntun fitsari a wando yayin dariya. Ya faɗakar kuma ya nishaɗantar da mutane sosai fiye da tsammanina.

Wanne salon rubutu aka fi sanin ki a kai, kuma mai ya sa ki ka fi amfani da wannan salon?

Salon zance da adon harshe. Amma bayan haka babu kalar salon da ba na amfani da shi yayin rubutana.

Mai ya ja hankalinki kan rubutun barkwanci?

Kasantuwata ma’abociyar tsokana da son wasa, hakan ya sa na fi kauri a wurin barkwanci da abin da ya shafe shi. Ta yadda ko haɗuwar farko muka yi da mutum a take zai gano tsokanata da kuma yawan wasan da nake yi da mutane, babba da yaro kowa nawa ne. Hakan ya ƙara mini ƙarfin gwiwar rubuta labarin barkwanci.

Menene ya bambanta rubutun barkwanci da sauran nau’ikan rubutu da marubutan Hausa suka fi yi?

Bambancinsa da sauran rubutu nishaɗin da ake saka ma’abota karatun labaran, domin a duk lokacin da suka karanta ire-iren labaran za su tsinci kansu a cikin farin ciki ko da suna cikin damuwa. Saɓanin wasu nau’ikan rubutu da har kuka suke saka mutum, wani lokaci kuma mutum ya wuni yana tsaki saboda abin haushin da mutum ya karanta, bayan ɓacin rai da baƙin cikin da wani zai fuskanta har wani ya dinga faɗar an tayar masa da hawan jini.

Yaya karɓuwar wannan salon na barkwanci da ki ke yi a wajen masu bibiyar rubuce rubucen ki?

Sosai ya karvu a wurin mutane, saboda kowa yana son abin da zai faranta masa fiye da abin da zai ɓata masa rai.

A ina ki ke samun hikimar ƙirƙiro da labaran barkwanci da ki ke rubutawa?

Kawai yanayina ne hakan. Sai wani lokaci da nake nazartar wani abu idan na gani a zahiri ko a yayin kallo.

Yaya ki ke ji a ranki game da yadda masoyan rubutunki suke fahimtar rubuce rubucenki?

Daɗi sosai nake ji a raina musamman idan na ji ana wata maƙala a kaina, ko kuma ana yin sharhin littattafaina da abin burgewar da ke ciki, Ina tsintar kaina cikin wani mayalwacin farin ciki sosai tamkar na je Kano a ƙasa ba takalmi.

Shin kina ganin ya dace a ce marubuci yana da wani keɓantaccen salo da ya kamata a ce an san shi a kai?

Sam wannan bai dace ba, saboda shi marubuci tamkar hawainiya ya dace ya zama, ta yadda a kowanne lokaci ya kan iya rikiɗa ya koma abin da ake so ya fito a cikin sifar labarinsa. Likita, ɗan’sanda, Malami, Talaka, Attajiri, kowacce riga ya so ya saka zai iya cire tasa ya saka ta abin da yake so ya yi rubutu a kai. Dalilin hakan ya sa nake ganin rashin dacewar zama da salo ɗaya ga marubuci.

Kin taɓa buga littafin ki ko a ‘online’ ki ke fitar da su?

Ban taɓa bugawa ba amma yanzu haka Ina shirye-shiryen bugawa, a cikin kwanan nan, in sha Allah.

Yaya ki ke ganin za a inganta kasuwancin littattafan adabi, don marubuta su iya samun amfani daga abin da guminsu ya ƙirƙira?

An tava min, kuma na ji haushi sosai dangane da hakan. Sannan matsalar ‘yan YouTube masu ɗaukar littafi su ɗora, wannan ya zama ruwan dare game duniya. Saboda ni kaina akwai wani littafina ‘Shagalalliya’ Ina tsaka da rubuta shi na tsince shi YouTube an fara ɗorawa. Takaicin hakan ya sa na dakatar da rubutunsa kuma har yau ban kammala shi ba.

Wanne alheri za ki ce kin samu ta dalilin kasancewar ki marubuciya?

Na samu alherai da dama irin waɗanda baki bai isa ya furta a irin wannan ɗan gajeren lokaci ba. Na sha samun alherai ta sanadin rubutu kama daga kuɗi, data, sutura da sauransu, bayan wanda nake katarin samu idan na ci gasa ko na siyar da littattafaina. Sannan na haɗu da mutane masu daraja ta sanadin rubutu, waɗanda ta silarsa ne kaɗai zan iya taka irin wannan matsayin kai-tsaye, har na tsayu inda na ga dama na je in da nake so.

Bangon littafin ‘Ɓarauniya Ce’

Wanne abu ne ya faru da ke a harkar rubutun adabi da ba za ki taɓa mantawa da shi ba, na daɗi ko akasin haka?

A baya idan aka yi mini irin wannan tambayar kai tsaye nake ce wa ban tava fuskantar wani ƙalubale sanadin rubutu ba, amma yanzu baki buɗe nake faɗar na shiga gagarumin ƙalubale a sanadin rubutu, sai dai kuma na jingine hakan a matsayin ɗaukaka ce ta janyo mini, wanda kowanne bawa dole ne a jarraba shi a duk halin da ya tsinci kansa. Alhamdu lillah Ina godiya ga Ubangiji da har ƙalubalen ya juya zuwa wata sabuwar ɗaukakar da ban yi zato ko tsammani ba.

Abin farin cikin kuma shi ne, nasarorin da nake yi a wurin gasa, sannan girma da mutuncin da mutane suke ba ni ta sanadin rubutu, ba ƙaramin faranta raina hakan yake yi ba. Ina alfahari da rubutu a ko’ina zan daki ƙirji na faɗi hakan har ma na yi tutiya da adabi Ina tinƙaho.

Wanne marubuci ko marubuciya ce madubinki a harkar rubutun adabi?

Ba ni da madubi a duk faɗin marubuta, face na ji sha’awar abin alherin da wata marubuciya Fauziyya D. Suleiman ta ke yi ta sanadin rubutu, wanda nima nake fatan na yi domin mu haɗu wurin samun ladan. Wato da yardar Allah nima wata rana Ina da sha’awar samar da wata gidauniya ta tallafa wa mabuƙata da waɗanda suka samu rayuwar su a cikin wani ƙunci. Wataƙila ko ta sanadin hakan mu samu rabauta a nan duniya da gobe ƙiyama.

Menene babban burinki na rayuwa?

Babban burina a rayuwa bai wuce na taka wani matsayi mai girma a cikin rubutu da adabi ba. Sannan na biyu na samu damar da zan tallafi na ƙasa da ni tun daga kan gajiyayyu, marasa shi, har ma da nakasassu masu wata tawaya a halittarsu. Abu na ƙarshe na mutu cikin aminci na rabu da kowa lafiya na je wurin ubangijina cikin salama.

Wacce karin magana ce ta ke tasiri a rayuwarki?

A kullum na zauna Ina tunanin rayuwata ta baya da wadda nake ciki har ma wadda zan yi a nan gaba. Na kan cicciɓi komai kacokam na ɗora a mizanin ‘Sara da sassaƙa ba ya hana gamji toho’.

Na gode.

Ni ma ina godiya sosai.