Haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka na haifar da moriya ga ƙasashen nahiyar

Daga SAMINU ALHASSAN

A tsakiyar makon nan ne kamfanin gine-gine na kasar Sin na CCCC ya kammala ginin hanyar motar kwalta mai tsawon kilomita 56.5, a yankin Oromia na ƙasar Habasha, wanda ya kunshi gina gadoji 4 masu inganci.

Sakamakon kammalar wannan muhimmin aiki, yanzu haka al’ummun dake yankin Oromia za su samu zarafin safarar albarkatun gona masu yawa da inganci da suke nomawa, da suka hada da Alkama, da barley, da ’ya’yan itatuwa zuwa kasuwannin birnin Addis Ababa, fadar mulkin ƙasar.

Ko shakka babu irin wadannan ayyuka na samar da ababen more rayuwa, waɗanda kamfanonin ƙasar Sin ke yi a sassa daban daban na nahiyar Afirka na da fa’idar gaske, suna kuma ƙara tabbatar da aniyar Sin da ma su kansu ƙasashen Afirka na yin tafiya tare, domin cimma nasarar kafa al’ummar bai ɗaya ta Sin da Afirka mai makomar bai ɗaya.

A yankin Oromia na Habasha, wannan aikin hanya baya ga taimakawa manoma da yake yi a fannin safarar albarkatun gonakin su, titin zai kuma share wata hanya ta inganta yawon shaƙatawa a yankin kudu maso gabashin Oromia, zai kuma samar da zarafin jawo ƙarin masu yawon buɗe ido na gida da na waje zuwa yankin.

Masharhanta dai suna jinjinawa irin waɗannan manyan ayyukan more rayuwa da kamfanonin Sin ke aiwatarwa a Habasha, musamman cikin shekarun baya bayan nan, inda bayanai suka nuna cewa, cikin shekaru 10 da suka shuɗe, kamfanin gine-gine na CCCC kaɗai, ya aiwatar da muhimman ayyukan more rayuwa a Habasha, da suka haɗa da babbar hanyar ababen hawa mai tsawon kilomita 85, wadda ta haɗa birnin Addis Ababa zuwa Adama, da sabon zauren karɓar baƙi na filin jirgin saman Bole dake Addis Ababa, da wasu yankunan masana’antu da dama, da suka hada da na Mekelle da Jimma.

Waɗannan ayyuka na ƙara shaida cewa, haɗin gwiwar Sin da ƙasashen Afirka, na ci gaba da zama muhimmin jigo, na cimma moriyar ƙasashen Afirka.