Yadda sakacin jami’an asibiti ya yi sanadiyar mutuwar tsohon Kwamishinan Neja

  • Mutum ne mai son ya ga na ƙasa ya taso

Daga BASHIR ISAH

Kanen marigayi Danladi Nadayebo, Usman Ndayebo, ya ce, rasuwar dan uwansa na da nasaba da sakacin ma’aikatan Asibitin Kwararru na Ibrahim Badamasi Babangida da ke Minna, babban birnin jihar.

A ranar Lahadi hatsarin mota ya rutsa da marigayin da misalin ƙarfe 7:30 na yamma a hanyar Suleja-Minna inda ya Allah Ya yi masa cikawa washegari Litinin da misalin ƙarfe 2 na rana.

Da yake bayani game da yadda abin ya faru, Usman ya ce yayan nasa (marigayin) ya isa Asibitin ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar da hatsarin ya faru, inda ya yi musu ƙorafin yana jin ciwon ƙirjinsa.

Ya ce babu wani ma’aikacin asibiti da ya saurare shi balle a bincika a gano musabbabin ciwon ƙirjin nasa har zuwa wayewar gari.

“Lokacin da aka kawo su asibitin babu ma’aikatan da za su sarrafa na’urar gwaji da ɗaukar hoto don gudanar da bincike a kansa,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa har zuwa safiyar Litinin, marigayin bai samu wata kulawa daga jami’an asibitin ba, sai bayan da tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Neja, Kuta Yahaya, ya zo ya saka baki cikin batun kafin aka fara duba shi.

Ya ce a daidai lokacin da suke ƙoƙarin ɗaukar marigayin zuwa Babban Asibitin jihar ne rai ya yi halinsa.

Da aka nemi jin ta bakinsa, Shugaban Asibitin na IBB, Isah Umar, ya ce bai san komai game da mutuwar Nadayebo ba.

“Ban san da haka ba, kuma ba ni da hurumin yin magana a kan haka,” inji shi.

A halin rayuwarsa, Marigayi Danladi Nadayebo ya taɓa riƙe muƙamin Editan Jaridar Leadership da muƙamin Daraktan Labarai na Gwamnan Jihar Neje da kuma muƙamin Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Neja.

Mutum ne mai son ya ga na ƙasa ya taso!

Da yake bayyana kaɗuwarsa da alhinin rasuwar marigayin a shafinsa na Facebook, Editan Jaridar Manhaja, Nasir S. Gwangwazo ya ce: “Wai Danladi Ndayebo yau babu! Mutuwa kenan! Ta ɗauki nagari, ta ɗauki mugu!

“Wannan bawan Allah ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarata a aikin jarida! Mun yi aiki a jaridar LEADERSHIP tare, inda na koyi abubuwa da yawa a wajensa!

“Labarina da shi yana da tsawo, saboda darussa na koya a ciki! Zumunci ba ya yankewa a tsakaninmu har ya zama ‘Director Press’ na Gwamnan Jihar Niger, daga baya kuma ya zama Kwamishinan Yaɗa Labarai!

“Mun yi tafiye-tafiye tare! Mutum ne mai haba-haba da jama’a! Mutum ne mai taimako! Mutum ne mai son ya ga na ƙasa ya taso!

“Allah Ya sa Ya girbi dukkan ayyukansa na alheri! Allah Ya yafe kurakurensa! Allah Ya kyauta makwancinsa! Allah Ya kyauta bayansa!”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *