An kaiwa tawagar Atiku hari a Borno

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A yau Laraba ne aka kaiwa ayarin motocin Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar hari a garin Maiduguri na Jihar Borno.

A cikin wani faifan bidiyo da aka gani a shafukan sada zumunta, an ga wasu gungun mutane suna ta gudu ta ɓangarori daban-daban yayin da ake ta harbe-harbe.

Wakilinmu ya ga yadda aka lalata motoci a cikin ayarin motocin Atiku a dandalin Ramat da ke Maiduguri babban birnin Jihar.

Kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku, Sanata Dino Malaye, ya ɗora alhakin harin kan jam’iyya mai mulki a Borno.

Melaye ya koka da yadda mutane sama da 70 ke kwance a asibiti.

“Sun so su hana mu gudanar da yaƙin neman zaɓen ne, kamar yadda muke magana, mutane 74 sun jikkata kuma an kwantar da su a asibiti.

Har yanzu APC ba ta mayar da martani kan zargin Melaye ya yi ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.