Ƙasar Sin ta kasance ta farko wajen yawaitar mutane masu hazaƙa a duniya

Daga CMG HAUSA

Yayin da ake gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da aka shigo da su ƙasar Sin na ƙasa da ƙasa karo na 5, cibiyar CCG ta gudanar da “dandalin tattaunawa kan yadda mutane masu hazaƙa suke kai komo da kuma samun ci gaba a duniya”, sannan an fitar da wani rahoto mai alaƙa na shekarar 2022.

Rahoton ya nuna cewa, daga cikin manyan ƙasashe 10 dake kan gaba a fannin takarar mutane masu hazaƙa a duniya, ƙasashen Turai da Amurka da na Asiya sun yi kankankan, yayin da cibiyar dake kula da taruwar mutane masu hazaƙa tana yaduwa daga Turai da Amurka zuwa yankunan Asiya.

Daga cikinsu yawan mutane masu hazaƙa dake nan ƙasar Sin ya kasance a kan gaba.

Mai fassara: Safiyah Ma