Alaƙar mawaƙa, marubuta, da ‘yan fim a siyasa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wani sabon salon yaƙin neman zaɓe da yanzu haka ya ke ɗaukar hankalin ‘yan Nijeriya musamman a nan Arewa, shi ne amfani da fuskokin fitattun ‘yan wasan kwaikwayo na masana’antar Kannywood a wuraren tarukan siyasa da cikin ƙungiyoyin yaƙin neman zave.

Dama dai filin yaqin neman zaɓe ya saba ganin mawaƙa suna baje kolin basirar su, don zuga ɗan takarar da suke so, ko wanda ya biya su, don ƙara kwarjanta shi a wajen jama’a, da kuma samun na ƙashin miya.

Sai dai mai yake janye hankalin matasa masu shirya finafinai da marubuta littattafan adabi da aka saba ganin su a lokeshen ko wuraren ɗaukar wasanni da situdiyo inda ake ɗaukar murya ko waƙoƙi na zamani, zuwa manyan tarukan siyasa da otal otal inda hanshaqan masu riƙe da muƙaman gwamnati da ‘yan siyasa suke gudanar da taruka da ganawa da magoya bayansu?

Idan an ce dama an saba ganin fuskar mawaqa irin su Rarara waɗanda siyasa ce ta ɗaukaka su har duniya ta san su, mai ya kai jarumi ko jarumar finafinan Hausa wajen taron siyasa? Wacce gudunmawa suke bayarwa, kuma wacce rawar za su taka a wajen?

Shugaban ƙungiyar masu shirya finafinai ta Nijeriya MOPPAN reshen Jihar Kano, kuma fitaccen ɗan wasa marubuci, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino, ya bayyana cewa waɗannan matasa suna cin kasuwar su ne, a wannan lokaci na kakar siyasa, don samar wa kansu abin da za su rufa wa kansu asiri.

Ganin cewa, yanzu kasuwancin finafinai ya ja baya, dole su nemi wata hanya da za su yi amfani da basirar su da sanannun fuskokin su da ake yawan gani a akwatin talabijin, domin tallata duk wani ɗan siyasa da ya nemi aiki da su.

Wannan kuma ya zo daidai da ra’ayin takwaransa na Jihar Filato, Darakta Auwal Y. Abdullahi, fitaccen mai ba da umarni ne a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood da ke Jos, wanda kuma har wa yau shi ne Mataimakin Shugaban Ƙungiyar MOPPAN a Jihar Filato, da ya ke ganin faɗuwar kasuwar finafinai ce ta tilasta ‘yan wasan bin ‘yan siyasa, don su samu na kashewa, domin sun saba da kashe kuɗi da walwala, kuma akasarin su da wannan harka suka dogara.

Tun a farkon fitowa takarar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, aka fara ganin gilmawar jaruman finafinan Hausa suna kai wa da komowa wajen taya shi yaƙin neman zave a cikin waƙoƙi ko a cikin fim, har ma a wasu wuraren yaƙin neman zaɓe.

‘Yan wasa irin Sani Danja da masu shirya finafinai irin su Abdul Amart Mai Kwashewa sun daɗe a wannan fage na shirya waƙoƙi ko dandazon mawaƙa don su tallata ‘yan siyasa ga masoyan su da ke kwaɗayin kallon fuskokin su a akwatin talabijin ko a zahiri.

Na baya bayan nan shi ne fitowa takarar Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ta ja zugar mawaƙa da masu shirya finafinai cikin yaƙin neman zaɓe da jan ra’ayin ‘yan qasa ga ɗan takarar da suka ce matashi ne mai ra’ayin cigaban matasa.

Dandazon waɗannan ‘yan wasan Hausa, ƙarƙashin jagorancin Mai Kwashewa, sun yi ta kewaya jihohin ƙasar nan, musamman jihohin Arewa, inda suka riƙa kwashewa da raye-raye da tallace-tallacen wannan ɗan takara da bai zo ya yi nasara ba, a zaɓen fitar da gwani da aka gudanar.

Tawagar mawaqa da ‘yan fim da Abdul Amart ya haɗa kuma suke camamarsu a wajen ‘yan siyasa ta ƙara buɗe idanun sauran masu shirya finafinai, mawaqa har da marubuta da ke ganin bai kamata a ci wannan kasuwar babu su ba. Duk da kasancewar a matsayin su na ‘yan Nijeriya suna da ‘yancin shiga siyasa da bin ra’ayin ɗan takarar da suke so.

Ballantana kuma sun daɗe suna tura wa ‘yan siyasa mota, sai sun samu nasara su tashi su buɗe su da hayaqi. Don haka ko takara ta kama a shirye suke su fita su ma a dama da su.

Shi ya sa ba mu yi mamaki ba, da muka ga fostocin wasu ‘yan wasan Hausa da mawaƙa lilliƙe a jikin gine-gine da kangwaye, su ma sun fita neman wasu muƙaman siyasa, irin su Gwamna da ɗan majalisa.

Ta iya yiwuwa irin wannan kishin ne tun a tashin farko a shekarar 2007 aka fara ganin shigar manyan ‘yan wasa irin su Hamisu Lamiɗo Iyantama, da ya nemi zama Gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin Jam’iyyar ADP ta wancan lokacin.

Mun ga irin tasiri da ɗaukakar da fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, jagoran ƙungiyar 13×13 waɗanda suke da ra’ayin amfani da basirar su da haɗin kansu, don cin moriyar romon dimukraɗiyya, wanda kuma a dalilin haka an ga canje-canje da dama a yanayin yadda siyasar Jihar Kano ke tafiya.

Shin za a iya cewa mawaƙa ƙarƙashin jagorancin Rarara su ma sun zama kanwa uwar gami kenan a siyasance? Mai wannan haɗin gwiwar mawaƙan siyasa da ‘yan wasa ke nunawa nan gaba?

Dauda Rarara da makusancinsa Rabi’u Gaya ba su amsa kiran da na yi ta musu don ba da manufarsu a kan wannan turba da suka hau kai ba. Haka ma Alan Waƙa Aminu Ladan Abubakar. Amma manazarta na ganin za a iya samun ƙalubale a gaba, idan aka yi la’akari da irin salon waƙoƙin zambo da yarfe da wasu mawaƙan irin su Rarara ke amfani da su a kan abokan adawar siyasar iyayen gidan su, ko kuma su kansu. Kamar yadda yanzu ake gani tsakaninsa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano.

Abdulrahman Yunusa, wani masanin harkokin siyasa a Jihar Bauchi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar kara dagulewar harkokin siyasa a Kano, matuƙar ba a ja wa wasu mawaƙa burki ba kan yadda masu mulki da ‘yan siyasa suka zama abin yi wa zambo da aibatawa ba.

Daga baya bayan nan kuma mun ga irin su fitaccen mawaƙi nan Aminu Ladan Abubakar (ALA) Alasan Ƙwalli, Nura Hussaini, Abba El-Mustapha, Bello Muhammad Bello, Lawal Ahmad, da kuma Bashir Lawandi Datti, da suka tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyu daban-daban suna neman masoya su zaɓe su.

Har ma kuma mun ga inda wasu jaruman Kannywood mata irin su Rashida Ibrahim da ta riƙe muƙamin mai taimakawa Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da shawarwari kan harkokin mata, da kuma Yahanasu Sani da ta samu matsayin mai taimakawa Gwamna Ganduje da shawarwari kan kasafin kuɗi, saboda kusancinsu da gidan gwamnati da kuma gudunmawar da suka ce sun bayar a yaƙin neman zaɓe da kafuwar gwamnati.

Ba ma a matakin jihohi ko ƙananan hukumomi ba, yanzu haka fitaccen jarumin nan Nuhu Abdullahi, tsohon mai fitowa a shirin talabijin mai dogon zango na Labarina shi ne yanzu Mataimakin Mai Kula da Walwalar Masu Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC. Matsayin da ko a ‘yan siyasa ma sai wane da wane.

Lallai babu shakka za a iya cewa, wannan siyasa ta zo wa ‘yan fim ɗin Hausa a matsayin Gobarar Titi a Jos, domin kuwa idan aka auna da abin da suke samu idan an gayyace su lokeshin za a iya cewa, bai kai cikin cokali ba.

A cewar Darakta Auwal Y. Abdullahi daga Jos, irin kuɗin da ‘yan siyasa suke kashewa ‘yan fim a yaƙin neman zaɓe, ya sa dole harkar fim ta ja baya a Arewa, domin kuwa ba kowanne mai shirya fim ko darakta ne zai iya yi musu wannan gatan ba.

A cewarsa, jarumi ne ko jaruma za a ɗauko hayarsu a kama musu Otal a ci da su abinci, a biya musu kuɗin mota, a kuma biya su don kawai jama’a su ga fuskar su a tare da shi. wannan dalilin ne ya sa darajar harkar film ta faɗi, suka rasa sana’ar da za su yi don samun irin kuɗin da suke samu kwatankwacin sa a harkar fim. Don haka ne suke amfani da sanuwar fuskokinsu wajen tallata ɗan takara ko jam’iyyar siyasa don samun kuɗin shiga ba tare da wahala ba.

Sai dai a wajen Mukhtar Musa Ƙarami wanda aka fi sani da Abu Hisham, Mataimakin Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Marubutan Jihar Kano (GAMJIK), da fitaccen marubuci kuma tsohon Sakataren Ƙungiyar Marubutan Hausa ta HAF a Jihar Kano, Kabiru Yusuf Fagge (Anka) suna ganin shigar masu fasaha irin mawaƙa, marubuta da ‘yan wasan Hausa, ba laifi ba ne domin kuwa wannan ita ce kaɗai hanyar da za su bi su samu kusanci da gwamnati ko ‘yan siyasa.

Suna ganin barin marubuta a ‘yan amshin shata ko ‘yan ƙwadago, waɗanda ba sa samun moriyar siyasa, sai ya biyo hannun wasu kafin a yaga musu, shigarsu siyasa ya zama wajibi.

Abu Hisham na cewa, ayyukan ƙungiyoyin marubuta da masu shirya finafinai, ba za su inganta ko su samu kulawar da ta kamata ba, idan ba sa yin siyasa, kuma siyasar ma ta zama mai ci wanda ke riqe da madafun iko, don in ba haka ba, ko izinin taro ku ka nema sai kun ga wariya da bambanci, ballantana in kuna neman wata alfarma a wajen gwamnati ko wani na kusa da su. Don haka ta ke ganin in dai aiki za su yi da basirarsu a biya su, ba wani abu ba ne, cigaban rayuwa ne ya kawo haka.

Muhammad Sani Abubakar, da aka fi sani da Ranjeet, marubuci ne kuma jarumi ne mai bayar da umarni a finafinan Hausa, shi ma yana ganin cancantar shigar ‘yan wasan Kannywood da mawaƙa cikin harkokin siyasa, domin a cewarsa idan laila ta ƙiya sai a koma basha.

Tun da harkar fim na neman mutuwa, kuma ‘yan siyasa sun fahimci irin ɗimbin masoya da magoya bayan da ‘yan fim ke da su, kuma dama jama’a suke nema, ai babu laifi su bi su don su samu abin da za su kula da rayuwarsu.

Ko da yake, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON na goyon bayan a shiga a dama da ‘yan fim, marubuta da mawaƙa, amma ya gargaɗe su da cewa, kada a zarme jiki da zuciya. Kada su zubar da mutuncin kansu da na sana’arsu, a duk inda suka samu kansu.

Ya ce, “Duk inda ka ke ka tuna da cewa wannan masana’anta ita ce ta mayar da kai abin da ka zama, wata rana za ka dawo. To, kada ka ci zarafin ‘yan cikinta. Kada ka ci zarafin abokan sana’ar ka.”

Abu Hisham a nasa vangaren nasiha ya yi wa marubuta da sauran masu fasaha, a daina tsayawa baya-baya, ko a riƙa dagewa da bin tsohuwar al’adar tafiyar da rayuwa, sai an fito an shiga jikin ‘yan siyasa ne kaɗai za a ci moriyarsu.

Shigar mawaqa da masu shirya finafinai ba baƙon abu ba ne, kamar yadda aka saba gani, tsakanin maigida da yaronsa. Amma yanzu da yaro ya taso yake son ya yi gogayya ko kafaɗa-da-kafaɗa da ubangidansa, wacce hanya za a bi don alaƙar ta yi daɗi, kuma kowa ya ci albarkacin kowa?