
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma sun shiga firgici a lokacin da aka gano gawar wani mutum mai shekaru 55 acikin wata mota da aka faka a harabar Majalisar Dokoki da ke Abuja.
Ana zargin mamacin mai suna Gaddafi Iwar kuma ɗan ƙabilar Tibi, lebura ne a wani wajen gini da ke wani sashe a majalisar.
A safiyar ranar Lahadi aka ga gawar tasa a wata mota ƙirar ‘Peugeot 406’ mai ɗauke da lambar rajista kamar haka: BWR-577 BF da misalin ƙarfe 9.
Haka kuma an gano cewa, an jima da ajiye motar a wajen kafin gano al’amarin.
Tuni aka garzaya da gawar zuwa asibitin da ke farfajiyar Majalisar, inda daga bisani aka kai ta zuwa Babban Asibitin Asokoro, amma aka ƙi karɓar ta saboda ruɓewa da ta fara yi, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa Zagazola Makama, wato ƙwararren mai sharhi akan harkokin tsaro.
Wani shaida ya ce, ƴan ƙabilarsa ne suka karɓi gawar, inda suka kai ta Ƙauyen Gbawu da ke iyaka da ƙwaryar birni (AMAC) da Kuje domin binne ta.
Al’amarin ya haifar da cecekuce game da makomar tsaro a yankin majalisar duba da yadda ake binciken mutane da ababen hawa gabanin ba su damar shiga.
