
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen mai sharhi akan al’amuran siyasa da ke zaune a Kano, Ibrahim Khalil Ɗan Shagamu ya haɗu da ajalinsa a gidansa da ke Kano bayan an masa kisan gilla, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici.
Rahotanni sun bayyana cewa, Ɗan Shagamu, wanda ke fitar da ayyukansa a ƙarƙashin Ɗan-Shagamu International, ya shahara da tsokaci a kafafen sada zumunta kan harkokin siyasa, addini da lamuran zamantakewa.
Ƙungiyar Amnesty International ce ta tabbatar da rasuwarsa a ranar Laraba, inda ta ce an samu gawarsa ne kwance cikin jini acikin gidansa. Ƙungiyar ƙare ‘yancin ta kuma yi tir da mummunan kisan da aka masa tare da kira ga hukumomin Nijeriya da su gaggauta gudanar da bincike kan dalilan mutuwarsa da kuma tabbatar da gurfanar da masu hannu a ciki a gaban doka.
“An yi masa mummunan yanka bayan makasan sun nuna masa fin ƙarfi,” inji Amnesty International.
Har yanzu ba a gano ainihin abin da ya sabbaba kisan ba, domin ‘yan sanda ba su fitar da cikakken bayani ko sanar da kame ba kan al’amarin. Saidai, wasu bayanai na Soshiyal Mediya da ba a tabbatar ba sun ce an yi wa Ɗan Shagamu mummunan kisa, ciki har da iƙirarin cewa an datse maƙogwaronsa, wato an masa “yankan rago”.
Amnesty International dai ta koka kan abin da ta kira da salon barazanar siyasa da wulaƙanci gabanin zaɓuka. Wannan al’amari ya jefa al’umma musamman a kafafen sada zumunta cikin jimami.
