An harbe mutumin da ya saci maggi da jan-baki

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jami’an tsaron ’yan sanda sun bindige wani da ake zargin ɓarawo ne a Awka, babban birnin jihar Anambara.

An ruwaito, an harbe wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe a tashar motar bas, ƙauyen Ifite da ke Awka bayan ya saci jakunkuna daga hannun masu zuwa da safe.

Majiya mai tushe ta ce, kayayyakin da aka gano a cikin jakarsa sun haɗa da jan-bakin Naira 600, ƙaramar wayar Nokia da kuma ƙwarorin maggi guda biyu da ya sace a hannun wasu mata uku da suke wucewa ta hanyar da safe.

ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, wadda aka sakaya sunanta, a garin Awka, ta ce an yi mata fashin waya da wasu kayayyaki, ta ce ‘yan ƙungiyar su uku ne kuma suka yi mata fashi da bindiga kafin a harbe ɗaya daga cikinsu.

“Ina dawowa daga aiki, sai wata yarinya da za ta je coci ta fito daga ƙofar masaukinsu, sai mutanen uku suka zo kusa da ni suka fara tambayar abin da nake da shi a cikin jakata. Yarinyar da za ta je coci ta gansu sai ta jefar da jakarta cikin daji. Suka duba jakata suka ga waya da kuɗi suka tafi da jakar.

“Sai ɗayar ta fara gudu zuwa masaukinta. Bayan na tattara jakata sai aka ce in gudu ba tare da na kalli bayana ba. Da gudu na nufi daji sai daya daga cikin ‘yan fashin ya bi ni, sauran biyun kuma suka bi ɗayar yarinyar. Ana cikin haka ne sai wani jami’in tsaron yankin ya fito ya harbe ɗan fashin inda ya kashe shi, yayin da sauran biyun suka gudu,” inji ta.

Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa, gawar wanda ake zargin ɗan fashin na nan kwance a yankin har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.

Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce uffan ba game da lamarin har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

By ukarofi