Dalilin da ya sa muka cafke Bobrisky a kan iyakar Nijeriya – Hukumar Shige da Fice

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar shige da fice ga ƙasa ta tabbatar da cafke Idris Okuneye, da aka fi sani da Bobrisky kan iyakar Seme yana ƙoƙarin ficewa daga Nijeriya.

A cikin wani jawabi da ya turo wa Manhaja, mai magana da yawun hukumar Kenneth Udo ya ce suna kan aikinsu ne na tabbatar da tsaron iyakokin ƙasar nan a lokacin da jami’an hukumar suka kama Bobrisky.

Hukumar ta ce tana kan binciken Bobrisky kuma da zarar ta gama, za ta miƙa shi zuwa ga humumomin da suka dace.

Daga nan ne hukumar ta ƙara ba da tabbacin cewa za ta cigaba da kula da iyakokin ƙasar nan yadda ya kamata domin wanzar da tsaro.

Manhaja tun da fari, ta rawaito muku cewa an kama Bobrisky ne a lokacin da ake duba takardar fasfo a kan iyakar Nijeriya da ƙasar Benin.

Sannan majiyarmu da ta buƙaci a sakaya sunanta, ta tabbatar mana cewa cewa an kama Bobrisky ne da tsakar dare ya shirin ficewa a asirce a lokacin da jami’in hukumar ya lura da sunan, daga nan ne ya sa aka sauko da shi ƙasa inda ya kwana sannan aka dawo da shi jihar Legas da safe.

A yanzu haka majalisar wakilan Nijeriya na gudanar da bincike a kan zargin da ake wa hukumar kula da gidajen gyaran hali ta ƙasa a kan shi Bobrisky ɗin.

Ana zargin Bobrisky ne da ba da cin hanci da kuma amfani da damarsa wajen samun kulawa ta musamman.

A kwanakin baya ne aka samu wata muryar da aka naɗa da ake yadawa a kafafen sa da zumunta, inda wani mai suna Martins Ortse (da aka fi sani da ɓeryDarkMan), ya zargi Bobrisky da bai wa hukumar EFCC cin hancin Naira miliyan 15 domin hukumar ta yi watsi da zargin da ake yi masa na safarar haramtattun kuɗaɗe.

Mai waccan maganar ta naɗaɗɗiyar muryar, ya kuma zargi Bobrisky da bin wasu hanyoyi wanda wani ubangidansa ya shige masa gaba wajen kauce wa zaman gidan yari na watanni shida da aka yi saboda cin mutuncin takardun Naira.

Sai dai Bobrisky ya musanta zargin muryarsa aka ji kamar yadda Martins Ortse, ya yi zargi wadda ta kai ga majalisar wakilai ta gayyace su, inda Bobrisky ya gaza zuwa.

By ukarofi