An kama boka kan zargin bai wa ’yan bindiga maganin bindiga

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta samu nasarar kama wani mutum mai shekaru 30 da ake zargi da yin asiri ga ’uan fashi da makami.

An cafke mutumin mai suna Cletus Effiong Bassey ne bayan samun sahihan bayanan sirri daga al’umma.

Punch ta wallafa cewa kakakin rundunar, DSP Timfon John, ta tabbatar da cewa an kama wanda ake zargin ne a daren 29 ga Yuli, 2025, a bukkarsa da ke ƙaramar hukumar Uruan.

DSP Timfon John ta ce, mutumin na bai wa ‘yan fashi magungunan kariya daga harbi da sauran nau’o’in tsafi.

DSP Timfon John ta bayyana cewa jami’an tsaro sun yi amfani da bayanan sirri wajen gano maboyar wanda ake zargi.

Bayan kama shi, rundunar ta gudanar da bincike a gidansa inda suka gano bindiga ƙirar gida, abin da ya ƙara tabbatar da zargin hulɗarsa da laifuffukan da suka shafi makamai.

A cewar ta, rundunar ta ɗauki wannan kame a matsayin ci gaba wajen yaƙi da ta’addanci da sauran manyan laifuka a jihar.

Binciken farko ya nuna cewa Bassey ya daɗe yana yin asiri ga ƙungiyoyin ‘yan fashi, musamman samar da maganin harbi.

A cewar jami’an tsaro, tsafin da ya ke yi wa ‘yan fashi yana sa su yi tsammanin ba za a iya harbe su ba, lamarin da ke ƙarfafa musu gwiwar kai hare-hare.

Haka kuma, akwai zargin cewa yana haɗa wasu nau’o’in tsafi ya ke ba mutane, wanda hakan na taimakawa wajen yaɗa ɓarna.

DSP Timfon John ta ce, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike don gano sauran waɗanda ke haɗa kai da Bassey.

Rundunar ta sha alwashin cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa duk masu aikata laifi sun fuskanci fushin hukunci.

By ukarofi