Rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen Abuja ta sanar da cafke wasu mata ’yan gida ɗaya da ake zargi da kitsa garkuwar ƙarya da zummar karɓar kuɗin fansa na Naira Miliyan biyar a wurin mahaifinsu.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Ta bayyana cewa sun samu tushen faruwar lamarin ne bayan da wani Innocent, ya kai rahoton ɓacewar ’yarsa mai shekaru 16 a ranar 18 ga Yuli, 2025.
Innocent ya shaida wa ’yan sandan cewa ’yar tasa ba ta dawo gida ba tun bayan da ta fita domin zana jarabawa a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Karu.
Mahaifin ya bayyana cewa bayan wani lokaci ne wasu suka kira shi da waya suna neman kuɗin fansa kafin su saki ’yar tasa.
“Nan da nan DPO ɗin ofishin Jikwoyi ya ƙaddamar da bincike, inda aka bibiyi lambar wayar da aka kira da ita har aka gano cewa waɗanda suka kira suna zaune a wani gida a Jikwoyi Phase II,” inji SP Adeh.
A cewarta, lokacin da aka isa gidan, an gano matashiyar da ake zargin an yi garkuwa da ita tare da wata mata a matsayin baƙuwa a gidan wani mai suna Mayowa Adedeji, suna cin abinci har da hira cikin natsuwa, babu wata alamar damuwa tattare da ita.
“ƙarin bincike ya nuna cewa yayarta ce da saurayinta yayar suka shirya makircin, tare da haɗin gwiwar matashiyar da kanta,” in ji Adeh.
An gano cewa yayar matashiyar ta kitsa makircin da wani saurayinta, inda suka tsara yadda za su ɗauke ‘yar uwarta su ɓoye ta a gidan abokin saurayin, yayin da yayar za ta ci gaba da zama a gidan mahaifinsu domin nuna kamar ba ta da masaniya kan abin da ke faruwa.
“Ita kuwa matashiyar da aka ce an yi garkuwa da ita, ta amince da wannan shiri, kuma ta yarda za ta zauna a gidan yayin da mahaifinta ke cikin tashin hankali,” inji sanarwar.
SP Adeh ta ce duka mutane huɗun da ake zargi suna hannun ‘yan sanda, inda nan gaba kaɗan a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala cikakken bincike.
