
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An sake samun hatsarin kwale-kwale a Jihar Sakkwato yayin da fasinjoji 10 suka rasu da ɓatar wasu 29 bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Gundumar Kojiyo dake Ƙaramar Hukumar Goronyo, ranar Lahadi.
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda inda ta ce an samu gagarumin rashi ga iyalai da al’ummar jihar.
Babban jami’in hukumar a Goronyo ya bayyana cewa kwale-kwalen, wanda ya matuƙar jigata, yana ɗauke ne da kusan fasinjoji 45 a lokacin da ya nutse a tsakiyar kogi.
An yi nasarar ceto mutane shida a raye yayin da aka baza komar cigaba da neman sauran guda 29.
Jami’in ya kuma ce, tawagarsu na cigaba da ƙoƙarin gano waɗanda suka ɓatan, sannan ana bai wa waɗanda aka ceto magani.
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa ta yiwu jido sama da kima ne dalilin faruwar iftila’in duk da cewa hukumomi sun sha gargaɗin masu gudanar da harkokin kwale-kwale game da kiyaye ɗaukar kaya ko mutane sama da kima.
