An kama ma’aurata kan shirya garkuwar ƙarya a Neja

Daga WAKILINMU

Rundunar ‘yan sanda a jihar Neja sun cafke wasu ma’aurata, Mohammed Mohammed da matarsa Sadiya Ibrahim Umar bisa laifin shirya garkuwar ƙarya da kawunansu a yankin Limawa da ke Minna babban birnin jihar.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna a ranar 15 ga Yuli, 2021 aka ba da bayanin cewa wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da Sadiya bayan ta shiga keke napep daga mararrabar Challenge da ke Maitumbi da nufin zuwa hanyar tsohon filin jirgin sama a Minna bayan da ta tashi daga wajen aikinta a Maitumbi.

Ana cikin haka ne washegari sai ga kiran waya ga mahaifinta inda aka buƙaci ya biya Naira milyan 5 a matsayin kuɗin fansa don a sakar masa ‘yarsa, amma daga bisani aka rage kuɗin zuwa Naira milyan ɗaya sannan aka buƙaci a kai kuɗin a ajiye a wani yanki na ƙauyen Rafin Yashi.

Tun ran 15 ga Yuli da aka sanar da ɓacewar Sadiya, sai a ran 21 ga Yulin ta komo gida, daga nan ‘yan sanda suka gayyace ta don ta amsa musi tambayoyi.

Da yake bayani kan lamarin, Mai Magana da Yawun ‘Yan Sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce Sadiya ce da kanta ta fallasa yadda suka haɗa baki da maigidanta wajen shirya yin garkuwar ƙarya da ita inda maigidan nata ya ɗauke ta zuwa ƙauyen Nugupi a yankin Paiko ya ɓoye ta a hannun wani abokinsa.

Jami’in ya ce Sadiya ta bayyana gaskiyar abin da ya faru ne bayan da suka matsa bincike a kanta.

Ya ci gaba da cewa shi ma maigidan nata ya faɗi gaskiya cewa shi ne ya karɓe wayar matarsa ya miƙa ta ga abokinsa Abdullahi, wanda shi ne ya kira waya ya kuma buƙaci a biya fansa, kuma shi ne ya karɓi kuɗin da aka bayar a madadin maigidan.

Ya ƙara da cewa, yanzu haka suna kan zurfafa bincike kan batun domin ganin an kamo Abdullahi, tare da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin baki ɗayansu a kotu bayan kammala bincike.