An kama matashi bayan yin kalamai a kan Aisha Buhari a soshiyal midiya

Daga BASHIR ISAH

Jami’an tsaro sun cika hannu da wani matashi kuma ɗalibi a Jaimi’ar Tarayya da ke Dutse, kan wasu kalamai da ya yi a soshiyal midiya game da matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari.

A cewar rahotanni, a watan Yunin 2022 Aminu Adamu Muhammed ya wallafa wasu kalamai a shafinsa na Tiwita, inda ya nuna Aisha Buhari ta bunƙasa bayan ta ɗanɗani dukiyar ƙasa, alhali ga talakawa na fama a ƙarƙashin gwamnatin maigidanta.

“Su mama an ci kuɗin talkawa an ƙoshi,” waɗannan su ne kalaman da aka ce Muhammed ya wallafa a shafin nasa.

Wani abokin matashin ya ce, Muhammed ya wallafa kalaman nasa ne saboda takaicin yajin aikin jami’o’i a wancan lokacin.

Yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta shafe wata takwas tana yi don neman cimma buƙatunta a wajen gwamnati.

Majiya ta kusa da ahalin matashin ta ce, an kama Muhammed ne ran 8 ga Nuwamba, 2022 a harabar jami’ar da yake karatu a garin Dutse.

Majiyar ta ƙara da cewa, sai da aka lakaɗa masa duka kafin daga bisani aka ɗauke shi zuwa Abuja inda aka ba shi taƙaitacciyar dama don ya kira mahaifinsa, Malam Adamu Shalele Azare a waya don sanar da shi inda ya ke.

An ce da farko iyayen sun zaci yana ofishin ‘yan sanda ne, daga baya suka gano yaron na hannun jami’an tsaron DSS ne.