An kama sojan da ya kashe ɗalibi a Kalaba

Daga WAKILINMU

Rundunar Sojoji ta Nijeriya ta bayyana cewa ta kama wani sojan da aka tura aiki a Gidan Yarin Calabar bisa zargin kashe wani ɗalibi da ke ajin ƙarshe a Jami’ar Kalaba mai suna Mr Gray Agbesu a ranar Juma’a, 9 ga Yuli 2021.

Daraktan sashen hulɗa da jama’a na rundunar, Brig.- Gen Onyema Nwachukwu, cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin da ta gabata, ya ce an cafke sojan ne a daidai lokacin da ya yi ƙoƙarin arcewa gudun kada a kama shi.

Ya ce yanzu haka sojan na tsare a hannun ‘Yan Sandan Sojoji kuma an soma gudanar da bincike don gano gaskiyar abin da ya auku wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗalibin.

Daga nan jami’in ya bai wa ‘yan’uwan marigayin tabbacin rundunarsu za ta binciki lamarin kisan kana ta gurfanar da sojan da ya yi kisan don ya fuskanci hukunci daidai da laifin da ya aikata.

Nwachukwu ya ce, “Kwamandan 13 Brigade ya ziyarci inda lamarin ya faru inda ya yi wa jama’ar yankin jawabi tare da ba su haƙuri kan abin da ya faru. Ya ba su tabbacin Rundunar Sojan Nijeriya za ta tabbatar doka ta yi aikinta.

“Kazalika Kwamandan ya ziyarci ‘yan’uwan marigayin don yi musu ta’aziyya, nan ma ya ba da tabbacin za a bi wa marigayin haƙƙinsa.”