An kama wata mata za ta kai wa ɗanta miyagun ƙwayoyi a gidan yari

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) sun kama wata mata da ake zargi da ƙoƙarin shigar da miyagun ƙwayoyi cikin Gidan Gyaran Hali na Ibara da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, domin kai wa ɗanta da ke tsare a gidan.

Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Jihar Ogun, Odukoya Olayinka, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce an kama matar mai suna Misis Iyabo Sowunmi ne yayin da jami’an tsaro ke gudanar da bincike a babbar ƙofar shiga gidan gyaran halin.

Ya ce jami’an sun gano wasu abubuwa da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne, waɗanda aka ɓoye a cikin leda ta garin abin sha.

A cewarsa, matar ta yi niyyar miƙa ƙwayoyin ga ɗanta mai suna Dare Sowunmi, wanda ke tsare a gidan gyaran halin bayan an yanke masa hukuncin kisa.

Bayan kama matar, hukumar ta ce an tsare ta tare da miƙa ta ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) reshen Jihar Ogun domin ci gaba da gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakin shari’a da ya dace.

Kwanturolan Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Jihar Ogun, Abioye Adesina, ya yaba wa jami’an tsaro bisa taka-tsantsan da suka nuna wajen gano ƙwayoyin kafin shigar da su cikin gidan.

Ya kuma buƙaci jama’a da su mutunta ƙa’idojin tsaro da aka tanada a gidajen gyaran hali domin tabbatar da tsaro.

Adesina ya yi gargaɗin cewa hukumar ba za ta lamunci safarar miyagun ƙwayoyi ko shigar da duk wani abu da aka haramta cikin gidajen gyaran hali ba, yana mai cewa duk wanda aka kama da karya doka zai fuskanci hukuncin da ya dace.

By ukarofi

Leave a Reply