An kashe ɗiyar Alƙali Ajumogobia a Legas

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

An kashe ɗiyar mai sharia Rita Ajumogbia Aribemchukwu a Legas da safiyar Laraba.

Mamaciyar wadda aka fi sani da Chuchu an kashe ta a gidanta da ke rukunin gidajen da ake kira Parkview Estate da ke unguwar Ikoyi a birnin Legas.

Wani ɗan uwanta da ya buƙaci a ɓoye sunan shi ya bayyana cewa an kashe ta ne a gidanta, inda a ka tsinci gawar ta a kusa da rukunin gidajen.

An fara zargi sabbin masu aiki da ta ɗauka aiki da basu jima ba. Domin alamu sun nuni cikin gidan kamar an so a goge jini.

Mai magana da yawun ƴan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar wannan lamari, kuma ya tabbatar yanzu haka a na tsare da mutum uku da ake zargi da aikata laifin.

Kafin mutuwar Aribemchukwu , ta kasance likita ce sannan bata jima da aure ba.

By ukarofi