
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani nau’in tashin-tashina ba yayin da ake gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya.
Gwamnan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin ƴan kasuwa, sarakunan gargajiya da malaman addini a Fadar gwamnatin jihar da ke Kano a ranar Laraba.
Abba Kabir ya ce, “zanga-zanga babu inda za ta kai mu. Ina kira ga waɗanda su ke ƙoƙarin aiki da ƴancinsu na yin zanga-zanga da su kaucewa nuna kowace irin halayya da gurɓatattu zasu yi amfani da ita.”
Ya ƙara da cewa, sun samu wani bayanin sirri da ke cewa wasu ɓata-gari na yin hayar ƴan daba don su tada hargitsi a jihar a lokacin zanga-zangar.
Kazalika, ya ce gwamnatin jihar ta na ƙoƙarin inganta tsaro a faɗin jihar. Don haka,
ba za ta lamunci lalata kadarorin gwamnati ko sata a shagunan al’umma ba.
