Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani matashi mai fafutuka a jihar Neja, Yahaya Mohammed-Usman, wanda aka fi sani da Sai Baba, ya yi kira ga gwamna Umaru Bago da ya gaggauta ɗaukar likitocin kula da cutar daji tare da kafa cibiyar kula da cutar daji a jihar domin daƙile ƙaruwar mace-macen masu kamuwa da cutar.
A cikin wani faifan bidiyo da ya yi wa gwamnan a ranar Litinin, Usman ya koka da yadda cutar ke ƙaruwa a faɗin jihar.
Mai fafutukar ya ce, abin takaici ne yadda ba za a iya samun wani ƙwararren masani a ɓangaren cutar kansa guda ɗaya a duk asibitocin mallakar jihar ba.
Ya ƙara da cewa, galibin masu fama da cutar kansa sai sun yi tafiyar kilomita da dama zuwa Abuja ko wasu sassan ƙasar kafin su samu kulawa.
ƙorafin Usman ya biyo bayan rasuwar ƙanwarsa Khadijah Bashir, wacce ta mutu sakamakon cutar a ranar Lahadi.
Ya ce: “A tsawon rayuwata ban taɓa ji ko sauraren wani labari mai raɗaɗi ba irin na rasuwar Khadijah Bashir [Ummi].
“Kansa ce ta kashe Ummi, cutar mai ban tsoro, mai raɗaɗi, mai kisan kai.
“Ummi ‘yar shekara 24 ce kuma da ƙyar ta kammala makaranta a matsayin ɗalibar lauya tana shirin zuwa makarantar lauya.
“Da jin wannan labari, sai hawan jini na ya ƙaru, kaina ya yi nauyi, idanuna suka yi ja suka yi jajawur, jikina ya yi rauni.
